Home Sashen Hausa Isah Ali Pantami ya zabtare kashi hamsin na kuɗin data da ƴan...

Isah Ali Pantami ya zabtare kashi hamsin na kuɗin data da ƴan Najeriya ke amfani dashi

Isa Ibrahim Pantami: Ministan sadarwa ya zaftare farashin Data a Najeriya

PANTAMI

Gwamnatin Najeriya ta sanar da zaftare farashin data da fiye da kashi 50 cikin 100 bayan umarnin da ta bai wa hukumar kula da kamfanonin sadarwar ƙasar ta NCC na fito da matakan aiwatar da hakan a hukumance.

Ministan sadarwa Dakta Isa Ibrahim Pantami, wanda ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter ranar Alhamis, ya ce matakin ya yi daidai da umarnin da ya bai wa hukumar ta NCC na bijiro da matakan rage farashin Datar domin sauƙaƙa wa jama’a.

“Yanzu za a riƙa sayar da Data 1GB a kan Naira 487, a maimakon N1000 da aka saba sayarwa a baya,” in ji sanarwar.

“Wannan ya samo asali ne daga wani rahoto da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta gabatar ga ministan bayan aiwatar da umarnin,” in ji wani mai taimaka Pantami, Mista Femi Adeluyi.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

A cewarsa, ministan ya ƙaddamar da wani kwamiti da zummar samar da sauƙi a amfani da Data, da ake sa ran zai ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2025.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da shirin a ranar 19 ga watan Maris na 2020 a Abuja.

Ɗaya daga cikin manufofin shi ne rage farashin Data zuwa Naira 390 daga nan zuwa shekarar 2015.

Ko gwamnati na da damar ɗaukar wannan mataki?

Wasu layukan Najeriya

Masana a ɓangaren sadarwa na ganin cewa gwamnati ba ta da hurumin ƙayyadewa kamfanonin sadarwa a ƙasar farashi, hasalima aikinta shi ne bayar da shawara a kan farashin da take ganin ya kamata a yi amfani da shi.

Wani aiki kuma da ake ganin shi ne ya rataya a wuyar hukumar kula da kamfanonin sadarwa ƙasar shi ne tabbatar da ƴan ƙasar sun samu sadarwa mai kyau, tare da kare haƙƙokinsu da kuma tabbatar da cewa kamfanonin ba su yi wani abu da ya sabawa doka ba.

Idan kuwa hukuma ta samu wani kamfani da yin wani abu da ya saɓawa doka, tana da damar cin tararsa, kamar yadda a shekarun baya-bayan nan gwamnatin Najeriya ta ci tarar kamfanin MTN biliyoyin daloli.

Abin jira a gani shi ne yadda kamfanonin sadarwar Najeriyar za su karɓi wannan al’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE? muazu hassan @ jaridar taskar labarai Gobe za a kai mahadi shehu Wanda yan sanda suka kawo daga Abuja...

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity By Bello Hamza, Abuja The group under the aegis of initiative for coalition and rights protection a not...

CUTAR KORONA, BABU WANI ILLA DA YA NUNA WA SHUGABA BUHARI BAYAN YIN RIGAKAFI KORONA.

CUTAR KORONA, BABU WANI ILLA DA YA NUNA WA SHUGABA BUHARI BAYAN YIN RIGAKAFI KORONA. Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren...

Bazamu sake yin yarje-jeniya da ‘yan bindiga ba saboda sunci amanar mu- Aminu Bello Masari

Ba Za Mu Kara Yin Sassanci Da ‘Yan Bindiga Ba A Katsina, Saboda Sun Ci Amanar Yarjejeniyar Sulhun Har Sau Biyu, Cewar Gwamna Masari Gwamnan...
%d bloggers like this: