Iran za ta biya dala 150,000 ga iyalan duk fasinjojin jirgin Ukraine da ta harbo

Iran ta ce za ta biya dala dubu 150 ga iyalan kowanne fasinjan da ya mutu lokacin da ta harbo wani jirgin saman Ukraine bisa kuskure.
Ofishin gwamnatin Iran kan harkokin shari’a ya ce adadin kudaden sun yi dai-dai da dokokin kasa-da-kasa.
Sojojin saman Iran sun kakkaɓo jirgin ne bisa kuskure yayin da ya tashi daga Tehran a lokacin da dangantaka tsakanin Iran da Amurka ta yi tsami kusan shekara guda da ta gabata.