Iran ta ce Amurka za ta ɗanɗana kuɗarta idan ta kai mata hari

Wani mai magana da yawun gwamnatin Iran ya ce Amurka za ta ɗanɗana kuɗarta matuƙar ta kai wa Iran hari.
Ya faɗi hakan ne bayan da aka ruwaito cewa a makon da ya gabata, Shugaba Trump yana tunanin kai hari kan babbar cibiyar nukiliyar Iran.
Mai magana da yawun gwamnatin Iran ya ce “wataƙila akwai yunƙurin kai wa Iran hari amma fa wannan ra’ayina ne ba na mai magana da yawun gwamnati ba.
“Ni a karan kaina ba na hasashen faruwar hakan. Ba na ganin akwai yiwuwar za su so haifar da matsalar tsaro a duniya da kuma yankin,” in ji shi.
Kalaman na Ali Babei wanda aka wallafa a shafin intanet mallakin gwamnatin Iran na zuwa ne bayan wani rahoto da jaridar New York Times ta buga da ke cewa Mista Trump ya nemi manyan mataimakansa kan sha’anin tsaron ƙasa su yi masa ƙarin bayani game da zaɓin da ake da shi, da kuma yanayin da za a iya kai wa Iran hari.
An bayar da rahoton cewa a ƙarshe Trump ɗin ya yanke shawarar dakatar da aniyarsa saboda haɗarin ruruwar rikici a Gabas Ta Tsakiya.