Iran Ta Yi Musayen Wata ‘Yar Leken Asirin Isra’ila Da Wasu Iraniyawa ‘Yan Kasuwa Uku

Jami’ar leƙen asirin ƙasar Isra’ila da Iran ta cafke shekaru biyu da suka gabata.

Iran Ta Yi Musayen Wata ‘Yar Leken Asirin Isra’ila Da Wasu Iraniyawa ‘Yan Kasuwa Uku

A jiya Laraba ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi musayen wata ‘yar leken asirin Isra’ila da aka kama a kasar da wasu ‘yan kasuwa Iraniyawa guda uku da ake tsare da su a wata kasa ta waje bisa wasu zarge-zarge marasa tushe.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar ta Iran ya ba da labarin cewa musayen fursunonin dai ta gudana ne a jiyan bayan da Iran ta sake wata ‘yar kasashen Birtaniyya da Australiya mai suna Kylie Moore-Gilbert wacce aka kama ta a shekarar 2018 da kuma yanke mata hukuncin zaman gidan maza na shekaru 10 saboda lafin leken asiri, a daya bangaren kuma aka sako wasu ‘yan kasuwa Iraniyawa guda uku da ake tsare da su a wata kasa ta waje.

A shekarar 2018 ne jami’an tsaron Iran suka kama Kylie Moore-Gilbert bayan ta shigo Iran da sunan gudanar da bincike na addini da kuma mazhabar Shia inda ta dinga gudanar da bincike da kuma tattaro bayanan sirri na bangaren tattalin arziki da ayyukan soji na Iran tana mika su ga haramtacciyar kasar Isra’ila inda bayan shari’ar da aka mata aka yanke mata hukuncin shekaru 10 a gidan maza.

Bayanai dai sun nuna cewa a shekarun baya ne kungiyar leken asirin Isra’ilan MOSSAD suka dauke ta aiki don tattaro musu bayanai a kasashen musulmi inda tsawon shekaru ta tafiya kasashen musulmi daban-daban da sunan gudanar da bincike kan addinin Musulunci saboda kwarewar da take da shi a wannan bangaren amma tana tattaro musu bayanan sirri har lokacin da dubunta ya cika inda jami’an tsaron Iran suka kama ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here