Home Sashen Hausa Iran ta haramta shigar da riga-kafin korona da aka yi a Amurka...

Iran ta haramta shigar da riga-kafin korona da aka yi a Amurka da Birtaniya ƙasarta

Iran ta haramta shigar da riga-kafin korona da aka yi a Amurka da Birtaniya ƙasarta
Ayatollah

Shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya haramta shigar da duk wata allurar riga-kafin korona da Amurka ko Birtaniyya suka samar.

Shugaban ya ce bai amince da su ba, Iran dai tana zaman tankiya da Amurka da Burtaniya na tsawon shekaru da dama.

Yayin wani jawabinsa ta gidan talbijin, Ayatollah ya yaba da ƙoƙarin Iran na samar da allurar riga-kafinta, ko da yake, ya ce kasar za ta nemo ƙarin allurar daga wasu nagartattun wurare.

Duk da yake bayaninsa bai fayyace abubuwa a fili ba, sai dai ya nunar da cewa da Amurka za su iya samar da allurar riga-kafi mai inganci, da cutar ba ta fantsama a kasar sosai kamar yadda ake gani yanzu ba.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: