Advert
Home Sashen Hausa Iran ta fara yin gwajin riga-kafin korona da ta samar

Iran ta fara yin gwajin riga-kafin korona da ta samar

Iran ta fara yin gwajin riga-kafin korona da ta samar

Iran

Iran ta fara yin gwajin allurar riga-kafin cutar korona da ta samar da kanta a karon farko.

Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun ce Tayebeh Mokhber, wata ‘yar babban jami’in gwamnati Mohammad Mokhber, ita ce aka fara yi wa allurar mai suna Cov-IranBlessing a yau Talata.

“Wannan saƙo ne ga Iraniyawa cewa muna da tabbas game da allurar da za mu yi musu, kuma idan akwai wata matsala iyalanmu ne baki ɗaya za su fuskance ta,” a cewar Ministan Lafiya Saeed Namaki.

Mista Mokhber ya ce ƙasar za ta iya samar da riga-kafin guda miliyan ɗaya da rabi a cikin ‘yan makonni.

Iraniyawa kusan 55,000 ne suka mutu sakamakon cutar, adadi mafi yawa kenan a yankin Gabas Ta Tsakiya. Kazalika, fiye da miliyan ɗaya ne suka kamu da cutar a ƙasar.

Shugabannin Iran sun ce takunkumin da Amurka ta saka mata ya sa ba za ta iya samun riga-kafin korona ba, duk da cewa takunkuman sun yi sassauci kan magunguna da kuma kayan agaji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

TSAKANINA DA GWAMNATIN KATSINA(kashi na uku)

  Kabir sadiq (Dan Abu) A baya na tsaya inda mukayi waya da ADC kuma yaje ya gaya wa maigirma gwamna yadda abun yake, shi Bafarawa...

“My political career ends with the governorship of Rt. Hon. Aminu Bello Masari”…..Muntari Lawal

The opening caption above is his replay to us when we proposed to him to aspire for governorship race in 2019. His closing remarks...

A 39-year-old man, Ahmed Abdulmumini, has been arrested by the Katsina State Police Command for alleged cyber-stalking.

According to the police, Abdulmumini’s arrest followed a complaint by Governor Aminu Masari’s Special Adviser on Domestic Affairs, Alhaji Ibrahim Umar. Umar allegedly told the...

Tsohon Ministan Noma Abba Sayyadi Ruma ya Rasu a Birnin London

Da Dumi-Dumi: Tsohon Ministan Noma, Alhaji Abba Sayyadi Ruma Ya rasu a Birnin Landan INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN Allah yayima Alhaji Abba Sayyadi Ruma rasuwa...
%d bloggers like this: