Advert
Home Sashen Hausa Instagram ya dakatar da shafin Ayatollah Khamnaei

Instagram ya dakatar da shafin Ayatollah Khamnaei

Instagram ya dakatar da shafin Ayatollah Khamnaei

Ayatollah Khamnaei

Dandalin sada zumunta na Instagram ya dakatar da wani shafin Faransanci wanda jagoran juyin juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei ke amfani da shi.

Kafofin yaɗa labaran kasar ta Iran sun ce hakan ya biyo bayan wani rubutu da ya wallafa, wanda a ciki ya bukaci matasa a Faransa su tambayi hukumomi shin me yasa shakku game da kisan kiyashi a yakin duniya na biyu ya zama laifi, shi kuma batanci ga Annabi Muhammad ya zama ‘yancin fadin albarkacin baki ?.

Kasashen duniya da dama sun yi Allah-wadai game da matakin hukumomin Faransa na goyon bayan zanen barkwancin da ake yi wa Annabi.

Har yanzu shafin na Instagram bai ce komai dangane da al’amarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Rumbun tattara wutar Lantarki na Najeriya ya lalace, don haka za a fuskanci matsalar wutar lantarki mafi muni

Rumbun tattara wutar Lantarki na Najeriya ya lalace, don haka za a fuskanci matsalar wutar lantarki mafi muni Rumbun samar da wutar lantarki a Najeriya...

Saraki Ga ‘Yan Nijeriya: Ramadan Makaranta Ce, Mu Siffantu Da Darussan da Muka Koyo

Saraki Ga ‘Yan Nijeriya: Ramadan Makaranta Ce, Mu Siffantu Da Darussan da Muka Koyo Daga Muhammad Abubakar, Abuja Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Dr. Abubakar...

EFCC ta kwato karin $153m daga wurin Diezani

EFCC ta kwato karin $153m daga wurin Diezani Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta sanar da kwato...

Yanda aka gudanar da Huɗubar Sallar Idi Daga Gidan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi

Yanda aka gudanar da Huɗubar Sallar Idi Daga Gidan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi Jaridar WalkiyaMay 12, 2021 Sallar Idi Daga Gidan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi Ɗaruruwan Al'ummar...
%d bloggers like this: