Inna lillahi wa inna liayhi raji’un: Sheikh Ahmed Lemu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
Allah ya yi wa tsohon Alkalin nan a jihar Neja rasuwa, wato Sheikh Ahmed Lemu. Ya rasu ne da safiyar yau Alhamis kamar yadda iyalinsa suka tabbatar.
Nuruddeen Lemu, shi ne ya bayyana hakan a madadin iyalin, inda ya ce za su sanar da lokacin yi wa mahaifin na su jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.