Advert
Home Sashen Hausa Injiniya Muttaka Rabe Darma Ya Kaddamar Da Littafin Da Ya Rubuta

Injiniya Muttaka Rabe Darma Ya Kaddamar Da Littafin Da Ya Rubuta

Injiniya Muttaka Rabe Darma Ya Kaddamar Da Littafin Da Ya Rubuta.

Injiniya Muttaka Rabe Darma, a ranar Juma’a 1 ga Afrelun 2022, ya kaddamar da Littafin da ya rubuta da hannunsa, mai suna ‘Pathway To Greatness The Katsina State Of The Future’ a turance, littafin mai kundaddaki guda biyar.

Littafin “Hanyar Da Za A Bi A Ciyar Da Jihar Katsina Gaba” a Hausance, ya kasu gida biyar; Book1, Book 2, Book 3, da Book 4, sai kuma Book 5 wanda yake kan hanyar fitowa, wanda kowane Kundi yana kumshe da muhimman abubuwa kunshe a cikinsa.

Kundin farko na Littafin, ya kunshi “Tsakure” a kan abubuwa daban-daban da littafin ya tattara, wanda ya kunshi tarihin jihar katsina da na dadaddin Sarakunar kasar hausa da gwamnatocinsu har ma da na wasu kasashe.

Kundi na biyu kuwa ya kunshi “Harsashin Ci Gaba” na yadda za a dora jihar bisa turba mai nagarta, tayadda za a magance wasu matsaloli da suka addabe ta muddin an bi su.

Kundi na Uku shi kuma ya kunshi “Ginshikin Ci Gaba” na bin wadancan hanyoyin ci gaba da aka gindaya sau-da-kafa, don jihar cimma gacin da ake bukata.

Kundi na Hudu ko ya kunshi “Tunanin Ci Gaba” na yadda jihar za ta kai matakin ci gaban da ya wuce yadda aka tunani, muddin dai gwamnati ta yi aiki da abubuwan da aka shimfida a littafin akai yadda ya dace, wanda daga nan za ta kai wani mataki na kololuwa irin na kasashen da suka ci gaba a duniya ko ma ya wuce su.

A yayin da yake gabatar da Littafin a taron, Injiniya Muttaka Rabe Darma, ya koka kan yadda ga hanyoyin za a bi a iya magance wasu matsaltsalun da jihar ta tsunduma cikinsu cikin sauki, amma rashin damuwar haka da kar6arsu tare da yin aiki da su daga gwamnati ya faskara a kawo karshensu; kullum sai abin da yai gaba.

Daga karshen taron, Darma, ya amsa tambayoyi daga manema labaru a kan littafin nasa da kuma abin da ya shafi takarar gwamnan jihar da ya rigaya da ya fito.

Daga karshe, ya raba kwafi-kwafi na kundaddakin littafin ga mahalarta taron a kyauta, daga bisani ya sake amsa wasu tambayoyin ‘yan jaridu a karo na biyu, a shiri na musamman.

Muttaka Rabe Darma tsohon shugaban hukumar rarar man fetur (PTDF) a gwamnatin Umaru Musa da zangon farko na Goodluck Jonathan ne. Haka nan kuma, yanzu haka shi ne shugaban gidauniyar nan ta tallafawa matasa da koyar da sana’o’in dogaro da kai “Pleasant Library And Book Club(PLBC)” a turance, kuma dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

KARYA AKE MA GWAMNA. ……Sakon a zabi wani Dan takara

Muazu hassan  @katsina city news Ana yawo da wani labari cewa, Mai girma gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello masari, ya bada umurnin a zabi wani...

Zaben Fitar da Gwani Amanar Katsinawa na Hannunku Daligate: Jobe 2023

Daga Bishir Suleiman @Katsina City News Duk tirka-tirkar da ake na fitar da yantakara a jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Katsina, babu zaben...

Soludo Imposes Curfew On Eight Local Government Areas In Anambra State

By Ejike Abana (ABS Government House Correspondent) Governor Soludo has imposed a 6pm to 6am curfew for commercial motorcycle riders, shuttle buses and tricycle riders...

Hukumar KASROTA Zata Fara Aiki Ranar 1 ga Watan Yuni A Katsina.

Daga Auwal Isah An bukaci al'umma jihar Katsina su fahimta, tare da goya ma ayyukan hukumar KASROTA baya. Shugaban kwamitin kafa hukumar Sani Aliyu Danlami ya...
%d bloggers like this: