INEC za ta wajabta amfani da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN a katin zaɓe.

 

Hukumar zaɓe ta kasa a Najeriya, INEC, na duba yiwuwar wajabta amfani da lambar shaidar zama ɗan ƙasa a rajistar katin zaɓe yayinda za a cigaba da yiwa mutanen rajistar katin zaɓe a makonni masu zuwa.

Wani jami’in hukumar ne ya tabbatar da hakan ga Jaridar The Punch da ke wallafa labaranta a Najeriya.

Hukumar ta ce amfanin da lambar ɗan ƙasa a rajistar katin zaɓe zai daƙile matsalar yiwa yaran da shekarunsu ba su kai ba katin zaɓe da maguɗi da dai sauransu.

Nan da ɗan lokaci kaɗan ake saran hukumar ta fito domin sanar da shawarar karshe da ta yanke a cewar Punch.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here