INEC ta sanar da ranar da za a yi zaɓen gwamna a Anambra

Hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da ranar da za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra da ke kudancin Najeriya.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ne a ranar 6 ga watan Nuwambar 2021.
A yanzu dai Gwamna Willie Obiano na Jam’iyyar APGA ne gwamnan jihar, kuma hukumar zaɓen ta sanar da cewa wa’adinsa zai ƙare a ranar 17 ga watan Maris ɗin 2022.