Indiya ta ba Najeriya tallafin rigakafin korona
Najeriya ta karɓi tallafin korona 100,000 daga gwamnatin Indiya a ranar Laraba.
Hukumar kula da kiwon lafiya matakin farko ta wallafa hoto a Twitter na sakataren gwamnati Boss Mustapha lokacin da yake karɓar rigakafin daga jakadan Indiya a Najeriya.
Sai dai gwamnatin Najeriya ba ta bayyana sunan kamfanin da ya samar da rigakafin da ta karɓa daga gwamnatin Indiya ba.