Inada yaƙini Insha Allahu! Allah zai lunka maku abinda kuka rasa- Sheikh Yaqub Yahaya Katsina;

Zaharaddeen Ishaq Abubakar
@katsina City News

Wakilin ‘yan’uwa Musulmi mabiya Sheikh El’zakzaky na garin Katsina ya je ziyarar jajen gobara a Babbar kasuwar katsina.

Ajiya juma’ne 26/3/2021 ‘yan kasuwar da sauran al’uma suka tarbi malamin bayan zagayawa da sukayi acikin kasuwar domin gani da ido, irin barnar da gobarar tayi.

Sheikh Yaqub ya nuna alhini gami da jan hankali cewa; akoma ma Allah a tsarkake dukiya da zukata, sannan a taimaka ma gajiyayyu (marasa karfi) Malamin yayi kira ga Gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafawa wadanda annobar ta shafa domin saukaka masu, yace koda Gwamnati zata kwashe duka kudin jihar ta gyara kasuwar lallai batayi asara ba, sabida gina kasuwa kamar gina al’uma ne, amfanin kudin Gwamnati kuma ta gina al’uma da su.

Da yake tsokaci a wajen, Kwamishinan Kasuwanci da masana’antu Hon. Abubakar Yusuf, Yayi Godiya da wannan ziyara ta jajantawa, yakuma tabbatarwa Malamin Irin kokarinda suke tun daga matakin Gwamnatin tarayya zuwa ta jihar katsina; inda yace “Mun dauki adadin suna da rumfunan da abin ya shafa kuma akwai hukumar bada agajin gaggawa ta kasa da tashigo cikin lamarin da Kwamitin Gwamnatin tarayya.

Yace; da yardar Allah Gwamnati zatayi iya kokarinta na ganin kowa ya koma wajen sana’arsa cikin dan kankanin lokaci shiyasa ma muka bada dama ga ‘yan kasuwa kowa yazo ya tattara abinda yayi saura domin muga filin wajen kuma muyi abinda yadace” inji kwamishinan.

Idan ba’a mantaba a satin da yagabata ne na ranar Litanin 22/3/2021 ne al’umar ta katsina suka wayi gari da wata irin gobara a babbar kasuwar ta cikin Birinin katsina wadda sukace basu taba ganin irinta ba. Gobarar wadda ta share tsawon awanni takwas tana ci, wadda ta janyo asarar dukiya ta biliyoyin nairori.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here