Media Forum Katsina ta shirya taron ƙarawa juna sani akan fasahar ƙirƙira ta zamani (CAREER IN TECHNOLOGY);

Taron wanda ya fara gudana a yau Al’hamis a Muhallin koyar da sana’o’i wato

(Katsina Vocational Training Centre)

A Unguwar Dutsen Amare dake cikin Garin Katsina, da misalin karfe 4 na yamma, zai ƙare gobe juma’a.

Taron ya samu baƙuncin Wani masani akan ƙirƙira ta kimiyyar zamani daga ƙasar Ghana kuma shugaban Kamfanin (USERLANCE AFRICA LLC) wato Mr Ishaq Abubakar, inda ya gabatar da Lecture akan ƙirƙira da hanyoyin da zaka samu kuɗi a Social Media.

Inda yayi bayani mai gamsarwa da kuma ƙarfafa matasa akan ɓunkasa tunani, dakuma samar da wani abu da zai kawo maka ci gaba.

Mr Ishaq ya kawo hanyoyi da dama da zaka samu tsabar kudi ta wayarka batare da ka shiga wani tsarin wala-wala da yake tashe na yaudara ba. Inda yabada misali da kansa yace “shi a yanzu haka a duk awa ɗaya yana samun kuɗi dala $150 wanda yayi daidai da Naira 75,000 na Najeriya” yace mafi ƙaranci kenan idan da yaso zai iya linka haka saboda akwai masu samun Dala 500 a duk awa guda.

Taron zaici gaba a gobe In Allah ya kaimu inda za’a gabatar da yanda ake buɗewa da tsara website da sauran kafofi na zamani da zasu amfani rayuwa kai tsaye.

Da yake tsokaci a wajen taron; Shugaban na Media Forum katsina Alhaji Basiru Abubakar ya nuna jin dadinsa ta hanyar yabawa da ƙokarin Matashin, dakuma jawo hankalin matasa akan maida hankali da fadada tunanin su, domin cin gajiyar abinda aka koya, yace; ” daga cikin matsalar da ke damun matasan ƙasar nan shine hadda talauci, shiyasa ma suke faɗama ko wane irin tsari na samun kuɗi da ya shigo batare da bincike ba” inda yabada misali da wala-walar INSEME da ta sanya mutane kuka a watannin da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here