Home Sashen Hausa Ina son mayar da Nigeria kasar da ta fi yaki da cin...

Ina son mayar da Nigeria kasar da ta fi yaki da cin hanci – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

Ina son mayar da Nigeria kasar da ta fi yaki da cin hanci – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana burinsa na mayar da Najeriya ƙasar da ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ba kuma ƙasar da aka fi yaƙi da matsalar.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin karbar rahoton kwamitin binciken tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Ayo Salami, kamar yadda mai ba shi shawara kan harakokin wasa labarai Femi Adeshina ya fitar da sanarwa a ranar Juma’a.

“Cin hanci da rashawa ya kasance a ƙasashe da dama. Wasu Gwamnatoci suna yaƙin da sauƙi wasu suna yaƙin koyaushe. Ina son Najeriya ta kasance cikin ƙasashen da ba su wasa da yaƙi da rashawa.”

Shugaban ya kuma ce “zuwa yanzu mun yi imani da alƙawalin mu kuma za mu ci gaba da jajircewa har sai Najeriya ta yi nasara a kan ɓarnar cin hanci da rashawa, da samun ci gaban tattalin arziki da kuma shawo kan matsalolin tsaro.”

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA

YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA Da misalin karfe 10:20 na safiyar yau Litinin, Alkalai uku sun...

PRESIDENT BUHARI RECEIVES FMR VP ARCH NAMADI SAMBO ON NIGER ELECTION.

PRESIDENT BUHARI RECEIVES FMR VP ARCH NAMADI SAMBO ON NIGER ELECTION. President Muhammadu Buhari receives the Former Vice President Arch Namadi Sambo on the Republic...

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE? muazu hassan @ jaridar taskar labarai Gobe za a kai mahadi shehu Wanda yan sanda suka kawo daga Abuja...

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity By Bello Hamza, Abuja The group under the aegis of initiative for coalition and rights protection a not...
%d bloggers like this: