INA SAMEER ISMA’IL MUSAWA?

Daga Wakilanmu
@ Jaridar Taskar Labarai

Ina Sameer Isma’il Musawa, wanda kwanan nan Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumeen Kabir Usman ya dakatar da nadin da yi masa na sarautar Sanyinnan Katsina, kuma Hakimin Musawa ya cire masa sarautar Yariman Musawa?

Duk wannan matsala ta same shi ne a kan wata murya tasa da aka dauka bai sani ba, yana wasu kalamai marasa dadi a kan Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da Sarkin Katsina da kuma hamshakin dan kasuwan nan, Alhaji Dahiru Mangal.

Taskar Labarai ta gano babu cewa wanda ya san inda Sameer yake, wasu sun ce yana Nijar, wasu kuma yana Legas, amma ‘yan sanda da ke bibiyar wayarsa ta hannu sun ce, yana Kaduna, kamar yadda wata majiya a Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar mana.

“Wayar karshe ta Sameer da muka bi a ranar 15/2/2021 yana Unguwar Kakuri a garin Kaduna”, in ji majiyarmu ta ‘yan sanda.

A martanin muryar Sameer da aka dauka wata yarinya ‘yar wani tsohon Sanata ce daga Jihar Katsina ta yi wani sakon muryar marar dadi tana fadin wasu kalamai wadanda ba su rubutuwa a kan Sameer da mahaifansa.

Muryar ta yarinyar ta yi maganganu da zarge-zarge masu muni wadda ake zargin daukar nauyin ta aka yi don ta rama abin da muryar Sameer ta yi a kan iyayen wadansu.

Wannan ya hassala daya daga cikin kannen Sameer, har aka yi zargin ya yi wa yarinyar barazana, ita kuma ta kai kara wajen ‘yan sanda aka kama shi. Har zuwa rubuta rahoton nan kanen na Sameer yana wajen ‘yan sanda tsare ana bincike.

WA YA NADI MURYAR TA SAMEER?

Binciken jaridar nan ya tabbatar cewa ‘yan’uwan matar Sameer da suke da ‘ya’ya biyar a tsakaninsu, kuma har yanzu tana aure a gidan Sameer, har ma tana juna biyu, sune suka nadi muryar.

An kuma nade ta da dadewa, wasu na cewa shekaru uku, wasu kuma na cewa shekaru biyar, lokacin da aka samu wata matsala tsakanin Sameer da Sarkin Katsina a kan nadin sarautar Yariman Musawa.

Sameer yana magana da kannen matansa ne bisa amana da yarda da kuma jin cewa ana magana ce ta ‘yan gida.

Maganar da aka dauka tana da tsawo, amma sai aka yanko daidai inda za ta biya bukatar da ake bukata aka watsa ta.

Sameer Isma’il matashi ne da Allah ya yi wa nasibin mu’amala da wasu manyan mutane masu bukatar irin aikin da yake masu na musamman. Wasu kuma na hulda da shi ne saboda kasuwanci ko harkar kwangila.

Ko wannan ibtila’in zai zamar masa karewar alkadarinsa? Lokaci ne zai nuna.
_______________________________________________
Jaridar taskar labarai na a bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com tana da yan uwa katsina city news da ke www.katsinacitynews.com da jaridar turanci zalla ta the links news dake www.thelinksnews.com. duk suna bisa shafukan sada zumunta na Facebook, you tube da sauransu. Duk sako a aiko ga 07043777779.081377777245.email katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here