Dukkan masu mukaman siyasa a Zamfara sun sauya sheka APC illa mataimakin gwamna. Mataimakin ya bayyana dalilin da yasa ba zai bi maigidansa APC ba Uwar jam’iyyar PDP ta lashi takobin kai Matawalle kotu Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Gusau, ya lashi takobin cewa zai cigaba da zama a jam’iyyar People’s Democratic Party PDP, duk da cewa gwamnan jihar, Bello Matwalle ya koma All Progressives Congress APC.

Dukkan Sanatocin Zamfara uku, yan majalisar wakilai shida da yan majalisa jiha 24 sun sauya sheka tare da gwamnan illa mataimakinsa.

Muhammad Gusau ya ce zai cigaba da kasancewa da PDP saboda jama’ar PDP suka tsaya da su lokacin da suke cikin bukata, rahoton Daily Trust.

A hira da manema labarai bayan komawar Matawalle APC, yace: “Zan cigaba da kasancewa da jam’iyyarmu da kuma mutanen da suka tsaya tare da mu lokacin da muke cikin bukata.

Gusau yace Matawalle bai nemi shawararsa ba kuma shi kansa jita-jita kawai yake ji.

Ya ce da gayya aka ki sanar da shi kuma wani shiri ne na haddasa kiyayya tsakaninsu, a wata riwayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here