Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Ya zuwa yanzu dai, al’amura na cigaba da wanzuwa game da wanene zai kasance sabon angon jam’iyyar APC a matakin jiha, inda kamar yadda aka sani mutun biyu ne ke kan gaba wajan ganin daya ya zama angon jam’iyyar a ranar 16/10/2021.

Sai dai bisa kokarin samun hakan, batutuwa da dama suna ta bayyana musamman game da Alhaji Bala Abu Musawa, wanda wasu ke ganin tamkar barazana ce ga takarar Dakta Mustapha Inuwa idan har ya samu zama shugaban jam’iyyar.

Akan wannan dalili yasa muka zurfafa bincike game da asalin alaka tsakanin Mustapha Inuwa da kuma Bala Abu Musawa, a siyasance da kuma zamantakewa tunda sun dade tare, kuma ma daga ina wadannan magangunu suke fitowa na cewa zai iya zama barazana akan Mustapha.

Alal hakiki duk wanda yasan Mustapha Inuwa to ya jalinci wannan batu na cewa wani na iya zama barazana kuma har Mustapha ya yarda da haka, shin daga ina wannan matsala take, kuma wace irin alaka ce take tsakanin Mustapha da kuma Bala?

Bincike ya tabbatar mana da cewa akwai alaka ta zamantakewa tsakaninsu, domin kuwa shi Bala Abu ya tashi ne a ‘yantumaki, a ya yin da Mustapha ya tashi a Danmusa, can ya yi firamari da sikandire kuma a can din aka haifi mahaifiyarsa, kafin daga baya ya koma Musawa, saboda haka akwai kyakkyawar alaka ta zumunci tsakanin iyayensu ba tun yanzu ba.

Domin jin tabbacin hakan, mun yi fama da Bala Abu don ya tabbatar mana da wannan batu sai ya ce, gaskiya baya da niyyar yin wata magana a daidai wannan gaba da wasu ‘yan siyasa ke neman haddasa rikici musamman ganin yana wannan takara, amma dai ya magantu daga baya.

“wato ni ban cika san yi magana akan irin wannan lamari ba, amma dai tunda ana magana ne akan Dakta Mustapha zan ce wani abu ko kadan ne, kamar yadda ka fada cewa muna da alaka ta zumunci haka ne wannan magana, iyayena da iyayansa akwai zumunci na tuntuni” inji shi

Ya kara da cewa, a siyasa tun lokacin gwamnatin Shema idan an taba Mustapha shi ne mutun na farko da ke shiga kafar sadarwa wajan kare shi da maida martani ga gwamnatin Shema, har zuwa lokacin da suka hadu a shugancin jam’iyya yana shugaba shi kuma yana mataimaki.

Bala ya cigaba da cewa,” Ni dan lele ne a wajan Mustapha da kuma gidansa domin duk abinda nake so shi ake yi mani, yanzu haka idan na kira shi a waya, abinda zai fara cewa shi ne, mai kuri’u da Motoci wannan abu yana yi mani dadi har gobe”

Haka kuma Bala ya ce lokacin da yake mataimaki karkashin shugabancin Mustapha ya samu dama so sai duk wani abu da za a yi kamar kwamiti shi Mustapha ke sawa gaba, kuma a samu nasara, kuma har zuwa yau din nan, ya ce Mustapha bai taba yin wata magana akan sa ba marar dadi, saboda haka yana mamaki masu nisanta shi da Dakta Mustapha musamman a siyasa.

Daga karshe Bala ya bayyana cewa ko a haka aka tsaya, ya san cewa shi dan uwa ne ga Mustapha tun kafin haduwarsu a siyasa, saboda haka shi na kowa ne, kawai dai wasu ne ke son sai sun shiga tsakaninsu, amma kuma ba za su yi nasara ba, kuma ya ce duk wanda ya san shi tare da Mustapha yasan wannan maganar da ya fada.

Wani bincike da muka gudanar mun gano cewa akwai wasu ‘yan takara da ke nuna cewa Bala Abu na sune su kadai, suna da yakinin cewa zai iya yi masu adalci idan zabe ya zo, shi ne kusan dalilin yin wadancan maganganu da Balan ya ce na siyasa ne, misali a gidan Ahmad Dangiwa da Dikko Umar Radda da kuma mataimakin gwamna Mannir Yakubu duk suna cewa Bala na su ne, amma shi ya ce na kowa ne ba na mutun daya ba.

Dangane da batun zaman sirri da suka yi da hamshakin dan kusawa kuma jigo a siyasa Alhaji Dahiru Mangal kuwa, Bala ya tabbatar da wannan zama na sirri da suka yi, sai dai ya ce ba zai yi karin bayani ba game da abubuwan da suka tattauna ba.

Daga bangaranmu kuwa idan hali ya bada zamu ji daga bakin sakataran gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa domin jin wace irin alaka ce tsakaninsa da Bala Abu Musawa?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here