Advert
Home Sashen Hausa Ina Da Tabbacin Masari Ya Cika Alkawarin Da Ya Daukar Wa Ilimin...

Ina Da Tabbacin Masari Ya Cika Alkawarin Da Ya Daukar Wa Ilimin Jihar Katsina, Cewar Alhaji Sabo Musa

Babban Mai Taimaka Wa Gwamnan Jihar Katsina, Kan Dawo Da Martabar Jihar Katsina, Alha Sabo Musa Hassan Ya Bayyana Cewa Kusan Duk alkawarin Da Gwamna Masari Ya Daukar Wa Al’ummar Jihar Katsina, kafin a zaɓe shi ya zama gwamna a 2015 na Tabbata Ya Cika Alkawarin. Domin Jihar Katsina Tana Da Mazabar Kansila dari ukku da sittin da daya, Babu Mazabar Da Gwamna Masari Bai Gina Makaranta Ba, Akwai Mazabar Da Aka Gyara Wa Makarantun Kusan Goma.

Alhaji Sabo Musa Hassan ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da aza harsashin gina azuzuwa shidda da Ɗanmajalisar Wakilai, mai Wakiltar Karamar Hukumar Katsina a Zauren Majalisar Tarayya ya duri aniyar yi a Makarantar Firamare Ta Dallatu Dake Sabuwar Unguwa, Bayan Gidan Rodi A Cikin Garin Katsina.

Babban Mai Taimaka Wa Gwamnan ya kara da cewa a 2015 da muka fita yakin Neman Zaɓe, Duk Lokacin Da Na Kaddamar Da Mai Girma Gwamna Yana Cewa idan kun Zaɓe mu, za mu Baiwa Ilimin yayanku Muhimmanci, ilmi, ilimi, Ilimi, Sannan Sauran Abubuwa, Na Tabbata Ya Cika Wannan Alkawarin.

Sabo Musa ya ci gaba da cewa Saboda Yadda Gwamnan Jihar Katsina ya Dauki ilimi Da Muhimmancin Gaske, Ya Gyara Makarantun Sama Da 2500, ba Kamar Yadda Ƴan Adawa Ke Cewa Gwamnati Fenti Ce, Ba Fenti Kawai Ake Yi Ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: