Advert
Home Sashen Hausa Ina Da Kwarewar Jagorantar Kasar Nan Zuwa Tudun Muntsira—Saraki

Ina Da Kwarewar Jagorantar Kasar Nan Zuwa Tudun Muntsira—Saraki

Daga Bello Hamza, Abuja

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, kuma daya daga cikin na gaba-gaba cikin masu neman jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugabancin kasar nan, Dakta Abubakar Bukola Saraki, CON, ya bayyana cewa, yana da sanin makaman aiki da kwarewar da ake bukata na jagorantar kasar nan tare da warware matsalolin da ake fuskanta. Saraki ya yi wannan bayanin ne a cikin jawabinsa a taron manema labarai da wakilan jam’iyyar PDP daga jihohin tarayya Nijeriya ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce, zaben shekarar 2023 nada matukar muhimmanci ga dukkan ‘yan Nijeriya, musamman ganin irin dinbin matsaloli da kalubalen da kasar ke fuskanta, a kan haka ya ce, yana da kyau a tabbagtar da an zabi jajirtacce wanda zai iya fuskantar matsalolin tare da samar da hanyoyin fita daga matsalar ba tare da rikicewa ba, ‘A don haka na kira wannan taron don in sanar daku dalilin da ya sa na shiga wannan takarar da kuma irin kwarewa na a fagen harkokin rayuwar al’umma Nijeriya’’ in ji shi.

Ya kuma bayyana irn nasarorin da ya samu a lokacin mulkinsa na gwamnan Jihar Kwara, inda ya samar da ingantacen tsarin kiwon lafiya ga al’umma jihar, “Za mu yi amfani da irin wannan samfurin wajen ganin ‘yan Nijeriya suna samun ingataciyar kiwon lafiya a dukkan matakai na gwamnati.

Daga nan ya kuma yi tilawar irin nasarorin da ya samu a zamansa na shugaban majalisar dattawa, inda suka tabbatar da bangaren gwamnati na aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata, ta yadda al’umma za su amfana, “Dukkan matsayin dana samu kai na a baya, na yi kokarin gudanar da ayyukan da za su amfani jama’ar kasa” in ji shi.

Daga karshe ya ce, “Zan zama tsani tsakanin matasa da dattawa, tsakanin Musulmai da Kiristoci, tsakanin Arewa da Kudu saboda ni cikakken dan Nijeriya ne” in ji shi.

Taron dai ya samu halartar ‘yan jarida daga kafafen watsa labarai da daman a ciki da wajen kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

“Ni na Sauke Haƙƙin da ya rataya a kaina saura da ku, Kuji tsoron Allah”…..Saƙon Ɗan takarar Gwamna, Sanata Sadiq Yar’Adua ga Delegate.

"Ni na Sauke Haƙƙin da ya rataya a kaina saura da ku, Kuji tsoron Allah".....Saƙon Ɗan takarar Gwamna, Sanata Sadiq Yar'Adua ga Delegate.   Zaharaddeen Ishaq...

Wata Sabuwa: Maryam Abacha Ta Maka Gwamna El-rufa’i A Kotu

Rahotannin da ya ke riskenmu yanzu sun bayyana cewa matar tsohon shugaban kasar Najeriya, Sani Abacha, wato Maryam Abacha ta maka Gwamnatin Jihar Kaduna...

Sanata Babba Kaita Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Sanatan Shiyyar Daura

Jam'iyyar PDP ta ayyana Sanata Ahmed Babba Kaita a matsayin Ɗan Takarar daya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Shiyyar Daura a Ƙarƙashin jam'iyar. Sanata Ahmed...

THE ONGOING CONSTRUCTION OF 330KVA TRANSMISSION LINE IN KADUNA WILL BE COMPLETED SOON #PositiveFactsNG

The Managing Director, Transmission Company of Nigeria-TCN, Alhaji Sule Abdulazeez says the ongoing construction of 330KVA transmission lines from kukandan to Mando power station...

EFCC Arrests 22 Suspected Internet Fraudsters in Asaba

Operatives of the EFCC, Benin Zonal Command on Sunday May 22, 2022 arrested 22 suspected internet fraudsters. The suspects: Promise Bassey, Raymond Diamond, Ifeanyi Anyasi,...
%d bloggers like this: