Ina Bukatar Cocin RCCG Da Su Ci Gaba Da Baza Reshinansu A Jihar Kaduna.” Inji Gwamnan Kaduna”

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Malam Nasiru El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce cocin RCCG ta ci gaba da baza rassa a jihar Kaduna. Gwamna El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban cocin RCCG na kasa, Fasto Adeboye.

Gwamnan na Kadunan ya ce, jihar Kaduna na bukatar addu’o’i domin shawo kan matsalolin da take fuskanta don haka tana maraba da faston.

Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya bukaci Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) ta ci gaba da gina rassa a dukkan fadin jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

“Gwamnan ya bukaci Fasto Adeboye ya ci gaba da gina rassa a jihar Kaduna domin jihar mu na bukatar addu’o’in ka, jihar mu na bukatar albarkarka.” A cewar sanarwar da tawagar watsa labaransa suka fitar bayan taron.

A cewar El-Rufai, RCCG ta kasance abin dogaro; alama ta hadin kan Nigeria da zaman lafiya da cigaba a jihar.

“Muna kuma bukatar albarka da addu’arka, a matsayin babban Malami, domin ka taimake mu da kallubalen da muke fama da shi a nan da kasa baki daya.”

Malamin addinin kiristan, wanda ya ce ya dade da sanin gwamnan tsawon shekaru. ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum mai tattausar zuciya.

Ya ce Allah ne kadai zai iya warware matsalar da ake fama da ita inda ya kara da cewa nasara na nan tafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here