Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, mai neman takarar shugabancin kasa a jami’iyyar APC ya ce idan ya zama shugaban kasa, WAEC za ta zama kyauta a Najeriya.

Tinubun ya ce hakan zai ba wa dalibai yan sakandire damar cigaba da karatun duk irin talaucin da su ke fama da shi.

Ya kara da cewa, iyaye za su samu sauki kuma su dena damuwa kan biyan kudin da a cewarshi ya ke hana yara da yawa cigaba da karatu.

DAILY TRUE HAUSA ta tattara cewar Tinubun ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin wata kungiya mai goya masa baya a jiya Talata.

“Mu za mu biya wa ‘ya’yanku kudin jarrabawar kammala sakandire, hakan zai sa ba a bar kowa a baya ba duk talaucin iyaye.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here