IN HAR NA ZAMA SANATA….UMAR TATA

Aikin Sanata guda biyu ne kacal. Daya a waje yake daya kuma a cikin gida. Na wajen shine kirkira da taimakawa wajen kawo tsare tsare da dokoki da sa ido kan bin doka don kyautata rayuwar al’ummar da kake wakilta da kasa baki daya. A nan gaskiya na shahara wajen kirkiro tsare tsare da dokoki don ci gaban jihar Katsina. Duk mai bibiya ta a wannan kafar sadarwar a shekarun baya zuwa yau ya san haka damar ce bata samu ba.

Tsohon dan takarar gwamnan katsina Abdullahi Umar tsauri TATA

Aiki na biyu shine kawo romon demokradiyya ga al’umma tasa. A kan wannan ne nike da tsari kamar haka. In Allah yayi mani Sanata na Katsina ta Tsakiya da yardar Shi da ikon Shi zan yi Constituency Offices guda biyu. Na farko a cikin birnin Katsina don kula da Batagarawa, Jibia, Kaita, Rimi, Charanchi da ita kanta Katsinar. Na biyu zan yi shi a Dutsinma domin kula da Kurfi, Safana, Danmusa, Batsari da ita Dutsinmar.

Kowane office za muyi mashi departments guda shidda:

a) SECURITY AND REFUGEE REHABILITATION: Wannan zai maida hankali ne wajen tsaro kamar yanda nayi rubutu a baya da taimakon yan gudun hijira.

b) WELDING, CARPENTARY AND WOODWORK DEPT: Wannan department din zai maida hankali ne wajen gyaran Makarantun da suka kware ko kofofi da windunan suka lalace. Zai maida hankali wajen gyaran tebura da kujeru da kuma yin sababbi da hadin kan LEAs 11 da Zonal Education Offices da ke cikin wannan zone.

c) BUILDING AND CONSTRUCTION DEPT. Wannan department din zai maida hankali ne wajen gine gine na masallatai, islamiyyu, makarantun boko, gyaran gidan Malamai na Allo da wajen karatun su, gyara da ginin gidan marayu, nakasassu da mahaukata, wajen shan magani da gina kwalbatoci da gyaran hanyoyi.

d) AGRICULTURE, WATER EXPANSION AND SANITATION: Shi wannan dept din zai maida hankali ne wajen taimakawa manoma na rani da damina da kayan aiki, gina earth dams, gini da gyaran boreholes.

e) EMPOWERMENT AND SOCIAL WELFARE DEPT: Wannan shine wurin da zamu yi aikin tallafawa marayu, matan aure da zawarawa, masu karamin karfi, masu neman aure da ire iren su.

f) YOUTHS AND SOCIAL REORIENTATION DEPT: Wannan dept na taimakon matasa ne a kan karatu, neman aiki ga wadanda suka gama karatu, daukar dawainiyar masu tafiya NYSC, JAMB da Empowerment training, bada tallafi ga masu bukatar shi a kan harkar su ta nema, kare mutuncin su, yaki da taaddanci da shaye shaye da dai sauran su.

Kamar yanda shawara ta kaya a jiya, biizinillahi zanyi takarar Sanata tare da neman yardar Allah da taimakon ku. Duk mai shirin taimaka ma wannan kuduri sai ya/ta shiga shafin Abdullahi Mati Usman ya aje sunan shi da lambar shi domin tunkarar wannan aiki. Ance mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka!

KATSINAD DAI ITA CE A GABAN MU!
Umar Tata tsohon Dan takarar gwamna ne a jahar katsina.kuma yana cikin dattawan jam iyyar APC a katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here