Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, idan Allah Yaso, za a kammala duk ayyukan da ake yi a tashar samar da ruwa ta Ajiwa zuwa tsakiyar shekarar 2022 mai kamawa.

Gwamnan ya fadi hakan ne bayan da ya kammala duba aikin. Ya kara da cewa aikin ya sami jinkiri ta dalilai da dama, manya a ciki na samar da injunan halba ruwan (Water pumps), wanda sai da aka nemo ainihin kamfanin da suka kera wanda suke a wurin tun kafuwar shi a shekarar 1974, suka zo suka nazarci yanayin wurin da kuma bukatar da ke akwai ta yanzu. Wannan bayanai dasu kamfanin na KBS dake kasar Jamus yayi amfani wajen kero sabbin famfunan da aka hada a Ajiwan da kuma wanda ake kan hadawa a tashar halba ruwan dake Kofar Kaura. Haka kuma, matsalar Korona ita ma ta taka rawa sosai wajen kawo tsaikon.

Ta bangaren yadda aikin yake tafiya kuwa, Alhaji Aminu Bello Masari ya nuna gamsuwa da yadda aikin yake tafiya cikin inganci da kuma nuna kwarewa.

Gwamna Masari ya bayyana cewa yanzu haka ana kan nazarin yadda za a kara girman madatsar ruwan ta Ajiwa domin samar da sama da Lita Miliyan ashirin ta ruwa. Kuma tuni kwararrun (Consultants) dake wannan aikin sun kammala shi kuma ‘yan kwangilar dake bukatar a basu aikin sun gabatar da bukatun nasu kunshe da kiyasin abinda aikin zai ci.

Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu FNIQS, Kwamishinan Albarkatun Ruwa Alhaji Musa Adamu Funtua da Dankwangilar Alhaji Salisu Mamman suka rufa wa Gwamnan baya yayin wannan ziyara.

Muna rokon Allah Shi bada ikon kammalawa cikin nasara domin al’ummar babban birnin jiha da kewaye mu wadatu da ruwan Famfo mu huta da ‘yan baro.

Ya Allah Ka kawo mana dauki Ka yaye mana wannan masifa ta ‘yan ta’adda da kuma ta tsadar rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here