Wani ɗan Najeriya ya shiga jerin wasu matasa 25 da Tarayyar Turai (EU) ta zaɓa a sassa daban-daban na duniya don su riƙa ba ta shawarwari kan harkokin ƙawancenta da ƙasashen duniya.

Matasahin da ya fito daga jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya an zaɓo shi ne da nufin sake ba wa matasa dama a harkokin diflomasiyar duniya.

An zaɓi Imrana Alhaji Buba na ƙungiyar Matasa masu yaƙi da ta’addanci wato Youths Initiative against Terrorism a ƙarƙashin wani shirin Tarayyar Turai na ƙarfafa gwiwar matasa.

Tarayyar Turai ta ce shirin mai suna Youth Sounding Board na da nufin ƙirƙirar wani sahihi kuma dawwamammen sauyi kan yadda ƙungiyar EU ke tuntuɓar matasa a cikin ayyukanta na haɗin gwiwa don raya ƙasashe.

Matashin ya shaidawa majiyar Blueink News Hausa cewa wannan dama ce a gareshi wajen isar da sakon matasa kai-tsaye da cimma duk wani bukatu na ci gaban matasa da kokensu.

Imrana Alhaji Buba ya shaida wa BBC cewa ko wanne matashi na da burinsa a rayuwa ko ra’ayi na ganin ya samar da ci gaba.

Sannan akwai lokutan da matasa za su ke son kawo shawarwari ko hulda da manyan ƙasashe da ke bada tallafi amma sai abin ya gagara.

Ya ce wannan dama ce a garesu domin ya tattauna har da manyan kwamishinoni tarayyar turan da wasu manyan-manya a nahiyar kan damammakin da bukatun matasa.

Matashin ya ce wannan matsayi da ya samu karin dama ce a gareshi musamman ga matasan da ke karkara don warware kokensu da dumbin matsaloli.

Me Shirin Ya Kunsa?

Shirin wata dama ce ga matasa a duk faɗin duniya domin bada shawarwari kan ayyukan da suka shafi nahiyar turai.

An zaɓi matasa daga sassan duniya da za su ke nazari da tsokaci kan shirye-shiryen nahiyar musamman ga matasa saboda jin ra’ayoyinsu.

Sannan matasa da aka zaba za su kasance kamar jagorori wajen bijiro da irin taimakon da za a ke ba wa matasa a sassan duniya.

Me Shirin Ke Son Cimma?

Ita kugiyar Turan na son tabbatar da cewa matasa da aka zaɓa na wakiltar sauran matasa duniya.

Cikin tsare-tsarenta da dokoki na son sani ko tafiyar da ra’ayoyin matasa.

Sannan akwai muhimman bayanai da ake so da shawarwari matasa sosai domin tabbatar da cewa an tafiyar dasu a kowanne bangare.

Shirin na shekara biyu ne amma akwai yiwuwar a kara shekarun idan wasu bukatun sun taso.

Majiyar Blueink News Hausa, BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here