An bayyana Ilimi, musamman na addinin Musulunci, a matsayin kashin bayan zaman lafiyar kowace al’umma.

Gwamnan Aminu Bello Masari ya bayyana haka a yau, a Kafur, wurin taron budewa da kuma hallanta Islamiyya da Masallaci wanda Gidauniyar Su’Ad Al’Abdul Jaleel dake kasar Kuwait ta gina ma al’ummar Kafur, Masari da kewaye.

Gwamnan, wanda ya dauki lokaci yana jaddada muhimmancin neman Ilimi da kuma taimakawa addinin Allah, ya ja hankalin jama’a da kada a raina girman aikin da za ayi ko karancin dukiyar da za a zuba wajen daukakawa da kuma yada kalmar Allah.

Gwamnan ya kara da cewa, hatta rashin Imani da rashin tausayin da ‘yan ta’adda suke yi mafi rinjaye Jahilci ne da kuma rashin sanin Addini.

A karshe, bayan godiya ga duk wadanda suka bada gudummawa wajen wannan aiki, Alhaji Aminu Bello Masari ya umurci Dangaladiman Katsina Hakimin Kafur Alhaji AbdurRahman Rabe Abdullahi da ya tabbatar da an kafa kwamiti mai karfi wanda zai rika kula da wannan domin al’umma su sami ci moriyar wurin yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here