Daga Tijjani Sarki

A kwanakin baya majalisar zartarwa ta jihar Kano ta karbi rahoton kwamitin kwararru a kan matsalar data shafi malaman makarantu a jihar,wanda sakataren gwamnatin jiha ya Kafa, a inda majalisar ta amince tare da bada umarni ga shugaban ma’aikata ta jiha ya tura duk wani ma’aikacin jiha dake da takardar shaidar koyarwa ta NCE, B.Ed, M.Ed da PhD zuwa makarantun jihar har ma da jami’oin jiha guda biyu a kididdiga ma’aikatan 4287 ne suke da wa ‘yanda suke da shedar koyarwa amma suna aikin daba na koyarwa ba.

Rahotanni na sun tabbar tuni hukumar ilimin bai daya ta jiha (SUBEB) ta fara aiwatarwa a inda ta fitar da jerin sunayen wa ‘yanda abin ya shafa tare da turawa hukumar kula da manyan makarantun sakandare ta jiha (KSSSSMB), ma’aikatan da abin da shafa ya hada da SSO(Wanda aka fi sani da inspectors),Quality assurance officers, matsayin da sai gogaggen malamin makaranta ne ke kawai, abin tambaya da duba anan wa zaiyi aikin su kenan? tunda dai dole ne ayishi. Koda yake masu aiwatar da aikin suna la’akari da cewa duk wanda yake acinkin albashin karamar hukuma Kuma yana da digiri ko da bana koyarwa bane to fa aikin ya biyo ta kansa.

Bayanin dake fitowa daga karamar hukumar birni (Kano municipal LEA) shine mutum chasa’in da bakwai (97) abin ya shafa wanda duk masu digiri na farko ne zuwa Sama har ma da shugabar bangaren kananan makartu ta sakandare( LEA head of Jss section) hanzari ba gudu ba dacan basu da aiki ne a LEA din ko kuwa yanzu in sun tafi wa zaiyi aikin su? shi dai wannan aikin na ba wan ba kanin ne domin hatta sakatororin riko na ilmi bai bari ba, Dan kwa guda tara daga cikin su ya shafe su (ko da yake daga baya an janye).

Ina Mai ganin cewa ko dai sun fahimci Umarnin a kaikaice ne ko Kuma sun riga mallam massalanci ne,Dan har yanzu dai babu wata takarda da gwamnati ta karkashin offishin Shugaban ma’aikata na jiha ta fitar wanda tayi bayani dalla-dalla game da aikin, ko da yake majalisar zartarwa ta kafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here