Home Sashen Hausa Ilhan Umar baƙar fata musulma ta sake cin zaɓen majalisar wakilai a...

Ilhan Umar baƙar fata musulma ta sake cin zaɓen majalisar wakilai a Amurika

Ilhan Omar ta sake cin zaɓe zuwa Majalisar Wakilan Amurka.

‘Yar Majalisar Wakilan Amurka Ilhan Omar ta sake lashe zaɓe a karo na biyu daga Minneapolis ta Jihar Minnesota.

Baƙar fatar kuma Musulma, Ilhan mai shekara 38 ta doke abokin takararta baƙar fata na jam’iyyar Republican, Lacy Johnson, inda ta samu kashi 64.6 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, a cewar kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Ilhan Omar ce ‘yar asalin Somalia da ta zama ‘yar Majalisar Wakilai kuma ɗaya daga mata Musulmai guda biyu da aka taɓa zuwa majalisar a 2018.

Tana ɗaya daga cikin wata tawaga da ake kira “Squad” ta mata guda huɗu da suka je majalisar a karon farko daga jam’iyyar Democrat.

Matan su ne: Rashida Tlaib da Detroit, Alexandria Ocasio-Cortez daga New York City, Ayanna Pressley daga Boston.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: