Ighalo ya yi bankwana da Man United

Ighalo

Odion Ighalo ya koma ƙungiyarsa ta Shenghai Greenland Shenhua bayan ƙarewar kwantiragin aro da ya je Manchester United.

Tsohon ɗan wasan Najeriya ya koma Man United a matsayin ɗan aro a Janairun 2020, wanda ya kamata kwangilar ta kare tun a watan Mayu.

Ighalo ya taka rawar gani a Old Trafford, ya zura ƙwallaye biyu a fafatawarsu da Derby County a gasar FA Cup da taka rawa a karawarsu na Europa da Club Brugge da LASK, kafin annobar korona ta dakatar da komai.

United ta tsawaita kwantiragi Ighalo, hakan ya ba wa ɗan wasan mai shekara 31 damar ci gaba da kasancewa da ƙungiyar zuwa wannan lokacin.

Shi ya soma zura ƙwallon farko a wasan kwata final da United ta yi nasara da ci 2-1 a hannun Norwich City.

Ɗan wasan dai ya haska a wasannin 23 na ƙungiyar, da zura kwallaye 5.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here