Inada Hujjojin da zan kare kaina, kuma sai nabi haƙƙina akan ɓata mani suna- Mahadi Shehu

Mahadi Shehu yayi karin haske akan zaman su na kotu a ranar Al’hamis 18/3/2021, Al’ƙalin Babbar Kotun tarayya dake kano A.alawes Allagoa ya Amince da bayarda Belin sa bisa Sharuɗɗa guda 2;

Sharaɗi na farko, ga wanda zai tsaya masa dole sai ya mallaki Gida acikin Birnin Kano ko fili, na biyu kuma za’a biya tsabar kuɗi Nera Miliyan 10, a yayin da ya kasa cika wannan sharadi kotu ta bada dama ga jami’an tsaro da su damƙashi izuwa gidan gyara halinka na Kurmawa dake Kano har sai ya cika wannan sharadi.

Katsina City News ta samu zantawa dashi bayan kammala zaman inda yake shedamana cewa an tuhume shi akan zarge-zarge guda 6 wanda kuma duka abu guda ne ake can-canzawa, Mahadi ya kara da cewa yanada cikakkiyar Hujja akan maganganun sa kuma idan har yayi nasara akan wan’nan shari’a shima zai shigar da ƙara akan ɓatamasa suna da akayi.

Ya kuke ganin wannan magana ta Mahadi Shehu?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here