“Idan kuka gujewa jama’a, Allah zaya tambaye ku, bama sai anje Lahira ba tun a nan Duniya zaku gani a’akwatin Zaɓenku” Sakon Gwamna Masari ga Ciyamomi da Kansilolin su…
Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsona City News 🗞️
Gwamna Aminu Bello Masari yaja hankalin Shuwagabannin ƙananan Hukumomi da Kansilolin su na jihar Katsina a lokacin da yake jawabi a wani taron karawa juna sani, wanda Ofishin Mai bawa Gwamnan Shawara a kan sha’anin tsaro hadin gwiwa da Ofishin Kwamishinan ƙananan Hukumomi da Masarautu na jihar Katsina ya shirya akan Dubarun shawo kan matsalar tsaro wa Zaɓaɓɓen Ciyamomi da Kansilolin su.
Taron na kwana biyu wanda aka gayyaci masana Shehunnan malamai daga ciki da wajen jihar Katsina domin gabatar da ƙasidu akan tsaro da kuma hanyoyin fahimtar juna a tsakanin al’uma.
A rana ta farko Shehin Malami Farfesa Usman Abubakar daga jami’ar Kwara ya gabatar da ƙasida akan muhimmancin Zaman Lafiya da yanda za’a iya gane ɓata gari a cikin al’uma, daga Bisani Dakta Muktar Alƙasim daga jami’ar Ahamad Bello dake Zariya, a sashin koyar da Aikin jarida ya gabatar da Ƙasida akan ‘Yansandan Al’uma (Cominity Policing) Yanda suke, aikin su ma’anar su, da kuma irin gudummawar da zasu iyabawa ƙasa wajen samar da tsaro a cikin Al’uma. Inda ya bayyana da bada shawarwari ga mahukunta akan muhimman batutuwa don magance matsalolin na tsaro.
Daga bisani kuma Kwamishinan’yansanda na jihar Katsina ya gabatar da Kasidar sa da turanci, shima akan yanda al’uma zasu iya taimakawa jami’an tsaro domin samun zaman lafiya.
A rana ta biyu, an gabatar da jawabai daga manyan baki, daga ciki akwai Babban Jojin jihar Katsina, mai shari’a Musa Danladi Abubakar, inda ya gabatar da jawabi akan muhimmancin Sulhu a tsakanin al’uma, ba tare da anje kotu ba. Yace duba da yanayin da ake ciki na Shari’u sun ma Kotuna yawa, kuma shari’a tana da jan lokaci, amma sun fara samar da Ofisoshin Sulhu na yankuna kuma abin zaici gaba saboda anga natijar haka, inji Mai Shari’a.
Bayan gabatar da Dukkanin tsare-tsare na wannan taro daga bakin Alhaji Ibrahim Katsina, wanda Ofishin sa ya shirya taron, sai Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Honorabul Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ga gabatar da jawabin godiya da kira ga Dukkanin wadanda suka samu zuwa wajen taron da suyi kokarin aiki da abinda suka saurara. A karshe Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya rufe taron da jawabi na Nasiha, jan hankli Nuni, gami da gargadi da Dukkanin mahalartan musamman Ciyamomi da Kansiloli, inda yace: “A wannan zamani, tsabar son zuciya da son kai yayi mana yawa, kuma wannan halin yana daya daga abinda ya ke kawo lalacewar al’amura,” sana Gwamna ya tabo dalilai da ke kawo rashin tsaro, inda ya tunasar da masu riƙe da madafun iko da suki tsoron Allah, yace “Dukkanin mu sai an tambaye mu, ranar lahira cewa mi mukayi, mi muka aikata ma wadanda muke jagoranta, hanyar gujewa wannan tambaya itace kayi abinda ya dace.” Inji Gwamna Masari.
Yace “madamar bamuyi abinda ya dace ba, to bazamu tsallake wannan tambaya ba, tun anan duniya ma, sai mun gani a akwatinan zaɓen mu.”
Taron ya samu halartar Manyan Hafsoshin tsaro na jihar Katsina, Kwamishinan’Yansanda, Kwamandan Nigerian Scurity and Civil Defence, Shugaban Rundunar Sojojin sama na jihar Katsina, Comtroller na Hukumar Kwastam, Shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa Shiyyar Katsina (Immigration) Kwamandan ‘Yan Sintiri na jihar Katsina, Wakilin Sarakunan Katsina da Daura, da sauran ɓangarorin al’uma. Inda aka ƙarƙare taron da bada shedar Certificate a nan take, a ɗakin taro na Local Government Service Commission dake hanyar Kaita Daura da Ofishin ‘Yan majalisu na jihar Katsina.