Idan har ban bawa ƙananan Hukumomi dama ba, to ni naci Amanar Damar da aka Bani……….cewar  Dakta Dikko Umar Raɗɗa.

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Dakta Dikko Umaru Raɗɗa DG SMEDAN

Mai neman Takarar Gwamnan Katsina a ƙarƙashin Inuwar Jam’iyyar APC, kuma shugaban ƙanana da matsakaitan masana’antu na Najeriya wato SMEDAN Dakta Dikko Umaru Raɗɗa yayi wata ganawa ta musamman da ‘yan jarida a ranar Lahadi goma ga watan Fabrairu a Babban Ofishin yakin neman zabensa dake kan titin Tudun Katsira, inda Radda ya bayyana manufofi, da Ƙudirorin sa domin gina jihar Katsina idan Allah ya bashi damar zama Gwamnan jihar.

Dakta Dikko Umaru Raɗɗa ya zayyano batutuwa da zai duba ya kuma maida hankali a kansu, da suka shafi, batun Ilimi, Lafiya, Noma,  Bunkasa tattalin arzikin jihar Katsina, da Uwa-Uba tsaro, wanda yace idan babu shi dukkanin wadannan Ƙudurorin nasa ba zasu cika ba sai da kyakkyawan zaman lafiya.

Radda ya sha alwashin samar da ingantaccen tsaro, wanda zai sanya kwanciyar hankali ga dukkanin al’ummar jihar, inda ya ce zai dauki matakin magance su, daidai da yanda ya samesu, saboda sulhu da danta’adda bai cika haifar da ɗa mai ido ba.

Dikko ya tabo batun tsarin gudanarwar na aikin gwamnati inda yace zai canza tsarin daidai da Zamani, a batun ilimi Dikko ya ce idan Allah yaso zai fito da wani kyakkyawan tsari da zai bada damar tsamo hazikai daga dalibai a kowane mataki domin karfafasu da biya masu tallafin karatu domin jihar taci moriyar su.

A tsarin Noma kuwa Radda yace “nayi digiri uku akan sha’anin Noma don haka zan yi amfani da ilimin da nake dashi ta wannan fanni domin samar da ci gaba na ban mamaki, kuma na zamanantar da harkar ta noma, domin muyi fice mu zama abin koyi ga sauran jihohi dama kasashen ketare.”

Da yake amsa tambayoyi game da batun sakarma kananan hukumomi mara, Dikko yace “Idan har ni ban bawa ƙananan Hukumomi dama ba, to ni naci Amanar damar da aka bani” Dakta Radda ya kara da cewa “Marigayi Ummaru Musa Yar’adua ya bamu cikakkiyar dama a lokacin ina Shugaban karamar hukuma, “‘Yar’adua yana sako mana kudin mu, cikin Asusun mu muyi abinda duk muka ga karamar hukumar mu na da bukatarsa. kuma bai taba sanya mana baki ba.” Inji Dakta ya kara da cewa, yasan dai Marigayi Ummaru Musa Yar’adua yayi wani tsari na tabbatar da cewa kowane shugaban ƙaramar Hukumar ana bibiyar sa, da aikin da yake domin tabbatar da yayi abinda ya dace.

Daga cikin Ƙudirorin na Dantakarar Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa ya sha alwashin haɓaka ƙanana da matsakaitan masana’antu domin bunkasa tattalin arzikin jihar, ta hanyar abinda jiha take dashi, da kuma gayyato ƙungiyoyi na ciki da wajen ƙasar. Dikko ya tabbatar wa al’uma cewa zai aje muƙaminsa na shugaban SMEDAN, idan har Dokar da take magana akan hakan ta tabbata.

A karshe Dikko yayi fatan Alkhairi ga al’umar jihar ta Katsina da fatan samun Nasara ga zabukan ƙanan hukumomi masu zuwa.

Zaku iya samun cikakkiyar Tattaunawar ta Bidiyo 📷 a shafukan mu, na yanar gizo www.katsinacitynews.com

Ko ku sauke manhajar mu a Play store idan kuka rubuta KATSINA CITY NEWS zaku ga Application din sai ku sauke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here