Idan Allah Ya yarda, za mu kammala ayyukan kyautata samar da ruwa a cikin birni da kewayen Katsina a watanni ukku na shekarar 2021 mai kamawa.

Idan Allah Ya yarda, za mu kammala ayyukan kyautata samar da ruwa a cikin birni da kewayen Katsina a watanni ukku na shekarar 2021 mai kamawa.

Idan Allah Ya yarda, za mu kammala ayyukan kyautata samar da ruwa a cikin birni da kewayen Katsina a watanni ukku na shekarar 2021 mai kamawa.

Gwamna Aminu Bello Masari ya fadi haka bayan kammala duba ayyukan da ake kai a wurare daban daban dake ciki da kewayen birni.

Wuraren da Gwamnan ya duba sun hada da gidan ruwa na Ajiwa a inda ya duba sabbin manyan famfunan halba ruwa da aka kawo daga kasar Jamus, sai kuma aikin kafa sabbin Injunan samar da wutar lantarki (4,200Kva Generators) da kuma na’urar daidaita wutar (transformer).

Ya kuma duba aikin gyaran cibiyar halba ruwan dake Kofar Kaura, a inda ya bayyana cewa sakamakon duk ayyukan da ake kai ya ta’allaka ne a kan wannan cibiyar domin ita ke halba ruwan zuwa duk inda ake bukata. Wannan cibiya dai tun da aka gina ta a shekarar 1974 ba a taba samun kular da ake bata ba a yanzu wadda ta hada da gina sabbin ofisoshin Ma’aikata.

Bayan nan kuma, Gwamna Aminu Masari ya duba manyan tankunan ajiya da kuma tura ruwa zuwa ga al’umma masa’antu da suke a Rafindadi, sha-taletale na hanyar gidan rodi sai kuma wanda yake a kan hanyar zuwa Dutsinma.

Wannan ayyukan dai su za su tabbatar da an amfana da ruwan dake tahowa daga Zobe da kuma Ajiwa.

Gwamnan ya nuna gamsuwar shi a kan yadda aikin yake tafiya tare da bada tabbacin cewa da zarar an kammala wannan aikin, za a fara kashi na biyu wanda zai hada har da fadada madatsar ruwan (Dam) ta Ajiwa.

Babban Manajan hukumar samar da ruwa ta jiha Alhaji Ibrahim Dasuki da kuma Shugaban kamfanin dake aikin Alhaji Salisu Mamman suka zagaya da Gwamnan tare da yi mashi gamsassun bayanai akan ayyukan.

Credit Abdulhadi Ahmed Bawa SSA Social Media

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here