Kada a bude boda, kaya zasu hauhawa kuma Korona za tayi tsanani, Manoman gida
Zaharaddeen Mziag@Katsina city news
Manoman Najeriya a ranar Laraba sun yi Alla-wadai da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na sake bude iyakokin Najeriya na kasa.
Sun bayyana cewa bude iyakokin a yanzu da kayan abinci ke hauhawa abune mai hadarin gaskiya.
Sun ce kasashe makwabta da suka dogara kan Najeriya wajen samun kayan abinci zasu shigo kasar kuma hakan zai sa kayan abinci ya sake hauhawa, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar manoman Najeriya (AFAN) Arch. Kabiru Ibrahim, ya bayyanawa DT a hirar wayar tarho cewa bude bodan zai saukaka fitar da kayan abinci daga Najeriya zuwa kasashe masu makwabtaka da mu.
“Kuna ganin yanzu ana noma ana girba amma duk da haka kayan abinci na hauhawa saboda wasu dalilai,… inaga idan aka bude iyakokin, abin da hadari, ” yace.
Manoman sun kara da cewa a tuna har yanzu akwai annobar cutar Korona kuma bari mutanen daga wajen sun shigowa Najeriya na iya kara harzuka kamuwar cutar a nan.
A ranar Talata ne Ministan kudi da tsare tsare ta bayyana yiyuwar Buɗe iyakokin ƙasar ga mamema labarai a fadar Gwamnatin Nijeriya bayan taron sati sati da ake gudanarwa a fadar Shugaban Kasar.
Shamsuna ta ce shugaban kwamitin da Gwamnatin ta kafa domin yayi duba akan lamarin Iyakokin kasar, Kwamitin ya kammala aikin sa kuma yana gab da mika Rahoton shi, sai dai Ministan bata Ambaci lokacin da kwamitin zai gabatar da Rahoton nashi ba.
Najeriya dai ta ayyana kulle kan Iyakokin ta ne a cikin watan Agustan Shekarar Dubu Biyu da Sha Tara, Inda akayi zargin cewa ana safarar makamai da miyagun kwayoyi ta kan Iyakokin na Najeriya.