ICPC na neman surukin Shugaba Buhari ruwa a jallo saboda almundahanar $65m
ICPC

Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ayyana Gimba Kumo, daya daga cikin sirikan shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin almundahanar $65m na kudaden samar da gidaje ga ma’aikata

A 2016 ne Mr Kumo, tsohon daraktan gudanarwa na bankin Federal Mortgage ya asuri yar shugaba Buhari a Daura da ke jihar Katsina.

Cikin wani jadawali da hukumar ta fitar, ICPC ta bayyana Mr Kumo tare da Tarry Rufus da Bola Ogunsola a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo saboda zargin tafka almundahana.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin ICPC, Azuka Ogugua, ICPC ta bukaci jama’a su gabatar mata da duk wasu bayanai da za su taimaka mata wajen gano inda mutanen suke.

“Duk wanda yake da wani bayani kan inda mutanen suke yana iya ba da rahoto ga hedikwatar ICPC da ke Abuja ko ofisoshinta na jihohi ko ma ofishin yan sanda da ke kusa,” kamar yadda aka rubuta a takardar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here