#GaskiyarLamarinNijeriya

Ko kun san cewa, a ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi na inganta harkokin yaƙi da ta’addanci a Nijeriya, Rundunar Sojojin Ƙasa ta kafa sabuwar makarantar horar da jami’ai dabarun yaƙi da ta’addanci a yanar gizo?

An kafa ma’aikatar ne a ranar 8 ga Oktoba, 2021, a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka fara da ɗaukar ɗalibai guda 20 da nufin tabbatar da cewa, sun samu cikakkiyar ƙwarewa a fannin surkullen aikata miyagun laifukan a yanar gizo, don bai wa Nijeriya da ‘yan Nijeriya tsaron da ya dace da su.

Wannan na daga cikin tsare-tsaren Gwamnatin Shugaba Buhari wajen tabbatar da cewa, an kawo ƙarshen matsalolin tsaro a ƙasar, musamman don kasancewar yanzu yaƙi da ta’addanci ya wuce batun a tsaya a ƙasa ko sama ko kuma ruwa kaɗai!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here