Yanzu yanzu: Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci Shugaban masu safarar kayan Abinci bisa dalilin rufe hanya da hana kai kayan Abinci zuwa Kudancin kasar nan.

Shugabancin Kungiyar masu Safarar Shanu da kayan Abinci bisa jagorancin Kungiyar Amalgamated Union of Foodstuff and Cattle Dealers of Nigeria (AUFCDN) yanzu haka suna ganawa da Jami’an tsaron farin kaya na. (DSS).

Babban Sakataren Kungiyar AUFCDN, Ahmed Alaramma, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Labour House, Abuja, a Yau Litinin din nan, yace Shugaban Kungiyar na kasa baki Daya Mohammed Tahir, yana ganawa Jami’an Hukumar ta DSS.

Alaramma ya bayyana cewa hatta Sojojin ma suna barazana ga membobin su da suke kan hanya Suna hana Mutane Safarar, sun kuma bukaci Gwamnati ta sa baki adaina yi masu barazana.

Kafin yanzu dai Kungiyar ta bayyana aniyar ta ta cigaba da yajin Aikin tareda karfafa tare hanya da hana safarar kayan Abincin zuwa Kudancin kasar nan.

Ya bayyana cewa zasu cigaba har sai Gwamnatin Tarayya ta biya masu bukatun su na biyan diyya ta Naira Bilyan Dari Hudu da Sa’bani da Biyar N475 billion a Matsayin rashin rayuka da Dukiyoyin da membobin su sukayi yayin zanga zangar nan ta #EndSARS da kuma fadan ƙabilanci da ya abku a kasuwar Shasha Ibadan, haka nan sun bayyana Bukatar cewa akwai Gate gate da ake sanya masu akan hanya ana kar’bar kudaden su ba bisa ƙa’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here