Hukumar  Tantance Kwasa-kwasai ta Najeriya ta, Tantance ƙarin sabbin Kwasa-kwasai 9 a Polytechnic Katsina

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Hukumar da ke kula da tsarin Karatu da Tantance Kwasa-kwasai ta Najeriya NCCE ta Tantance ƙarin wasu kwasa-kwasai guda tara da za’a fara karantar dasu a Makarantar Kimiyya da fasaha ta Hassan Usman (Hassan Usman Katsina Polytechnic).

Biyo bayan Ziyara da Duba bangaren sabbin Kwasa-kwasan, d wakiliyar NCCE daga Babban Ofishin hukumar daga Abuja da ‘yan tawagar ta suka yi, inda suka duba sabbin gine-gine da kayi a makarantar gami da jinjinawa yanda ake gudanar da karatu da bada wasu shawarwari d zasu taimaka domin cigaban Ilimi a jihar Katsina da ma ƙasa baki daya.

Da yake maida jawabi, a madadin Hukumar gudanarwar ta makarantar Hassan Usman Katsina Polytechnic, Dakta Mudi Kurfi, ya godewa hukumar, kwarai da gaskiya na irin yanda makarantar ta samu kyakkyawar kulawa da bada shawarwari da zasu amfani makarantar da ɗalibai, inda ya sha alwashin dauka da aiki da duk wata Shawara da hukumar ta bada, domin fara karatun sabbin Kwasa-kwasan a kan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here