Hukumar NDLEA Ta Kama ‘Yan Bindiga Da Manyan Makamai A Katsina da Benue

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), sun kama ‘yan bindiga uku; Adamu Shehu, Tukur Mohammed da kuma Ibrahim Suleiman yayin wani hari da ‘yan bindigan suka kawo a jihar Katsina, dauke da bindigogi kirar AK 47 da wasu muggan makamai.

Kazalika, hukumar ta kama makerin makamai, Celestine Chidiebere Christian inda aka same shi da babban bindiga kirar G3 dauke da harsashi mai lamba 7.62mm guda 78 tare da fankon kokon harsashi a yayin da yake kokarin safarar makaman zuwa Jos, jihar Filato.

An gabatar da wadannan kámen ne a shingen bincike (check point) a jihohin guda biyu inda jami’an hukumar suke tsai da ababen hawa su bincike su dangane da miyagun kwayoyi.

Yayin da jami’an hukumar na jihar Benue suke mika makaman da aka kama da kuma mai laifin ga shugaban hukumar, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, a ofishin hukumar dake birnin tarayya Abuja, shugaban ya bayyana cewa hukumar sa za ta cigaba da bada kaimi wajen aiki da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da doka da oda.

“Mu a NDLEA zamu cigaba da yin iya karfin mu tare da jami’an mu don ganin mun dakile safara miyagun kwayoyi zuwa ga masu laifi ta hanyar toshe hanyoyin da kwayoyin suke isowa gare su. A saboda haka, baza mu yi kasa a guiwa ba wajen taimakawa sauran hukumomin tsaro musamman ma rundunar sojoji don ganin mun tabbatar da zaman lafiya da doka da oda” inji Janar Marwa.

A cewar sa, jami’an sintiri na hukumar sun kama ‘yan bindiga uku a yayin da suke aiki a karamar hukumar Malumfashi na jihar Katsina a ranar 5 ga watan Agusta a kan hanyar su daga Karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna zuwa Kankara na jihar Katsina don aiwatar da ta’addanci. An kama mota kirar Toyota Corolla mai lamba TRK 149 AE, tare da bindigogi uku kirar AK 47 da kuma harsashi mai yawa, layoyi daban daban, zobe masu yawa, kudade da wasu abubuwan na daban. Marwa yace tuni yayi umurni da jami’an su mika masu laifin ga rundunar sojoji a jihar Katsina don cigaba da bincike.

A yayin da yake magana akan mai laifin da aka kama a jihar Benue, Janar Buba Marwa yace an kama mai laifin ne a ranar 4 ga watan Agusta da misalin karfe 6:30am a wata motar fasinja mallakar Kamfanin CHI-Boy a kan hanyar Onitsha zuwa Jos lokacin da aka tsaida motar don bincike. A yayin da ake binciken ne aka ci karo da akwatin karfe wanda aka walde shi ta ko ta ina a cikin motar. Bayan an tambayi na waye ne, kai tsaye mutumin yace nasa ne.

“Bayan da aka dauki akwatin zuwa ofishin hukumar NDLEA na jiha tare da wanda ya yi ikirarin mallakin ta, an bude akwatin da na’urar yanka karfe “Filing Machine” inda aka samu kerarren bindiga G3 dauke da harsashi 78 mai lamba 7.62mm da kuma fankon gidan harsashi. Kai tsaye sai na nemi a kawo Celestine Chidiebere zuwa nan Abuja lura da manyan makaman da aka kama da yayi ikirarin shi ya kera su.

Janar Buba Marwa ya jinjinawa jami’an hukumar na jihohin Katsina da Benue saboda kokarin su da dagewa akan umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kawo karshen shaye shaye da kuma tsare kasar daga miyagun mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here