Advert
Home Sashen Hausa Hukumar NDLEA Ta Kama Mutane 43 Da Ake Zargi Da Fataucin Miyagun...

Hukumar NDLEA Ta Kama Mutane 43 Da Ake Zargi Da Fataucin Miyagun Kwayoyi, Ta Kuma Kwace Koyoyi Da Nau’insu Yakai 581.702kg A Jihar Kano

Hukumar NDLEA Ta Kama Mutane 43 Da Ake Zargi Da Fataucin Miyagun Kwayoyi, Ta Kuma Kwace Koyoyi Da Nau’insu Yakai 581.702kg A Jihar Kano

Daga Abdullahi Musa Sokoto

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta ce ta kame mutane 43 da ake zargi da fataucin muggan kwayoyi a watan Janairu.

Dokta Ibrahim Abdul, Kwamandan NDLEA a jihar, ya fadi haka ne a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a Kano.

Mista Abdul ya ce an cafke wadanda ake zargin a wurare daban-daban a cikin jihar biyo bayan gudanar da aiki da jami’an rundunar suka yi.

Ya bayyana cewa a yayin gudanar da ayyukansu daban-daban, rundunar ta sami nasarar cafke kilogram 581.702 na ganyayyaki da gari daban-daban a fadin jihar.

Ya da cewa, a cikin watan Janairun da muke ciki, sun sami nasarar cafke kilogram 533.553na wiwi, kilogram 48.052 na Psychotropic da kuma kilogram 0.097 na hodar iblis.

Mista Abdul ya ce a tsakanin wannan lokaci, rundunar ta yanke hukunci a kan wasu mutane hudu da ake zargi a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.

Mista Abdul ya ce an samu nasarar ne sakamakon namijin kokarin da jami’an NDLEA suka yi da kuma goyon bayan masu ruwa da tsaki daban-daban.

Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan nadin Birgediya-Janar mai ritaya, Buba Marwa a matsayin Shugaban hukumar, yana mai cewa ta fara samar da kyakkyawan sakamako.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

TSAKANINA DA GWAMNATIN KATSINA(kashi na uku)

  Kabir sadiq (Dan Abu) A baya na tsaya inda mukayi waya da ADC kuma yaje ya gaya wa maigirma gwamna yadda abun yake, shi Bafarawa...

“My political career ends with the governorship of Rt. Hon. Aminu Bello Masari”…..Muntari Lawal

The opening caption above is his replay to us when we proposed to him to aspire for governorship race in 2019. His closing remarks...

A 39-year-old man, Ahmed Abdulmumini, has been arrested by the Katsina State Police Command for alleged cyber-stalking.

According to the police, Abdulmumini’s arrest followed a complaint by Governor Aminu Masari’s Special Adviser on Domestic Affairs, Alhaji Ibrahim Umar. Umar allegedly told the...

Tsohon Ministan Noma Abba Sayyadi Ruma ya Rasu a Birnin London

Da Dumi-Dumi: Tsohon Ministan Noma, Alhaji Abba Sayyadi Ruma Ya rasu a Birnin Landan INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN Allah yayima Alhaji Abba Sayyadi Ruma rasuwa...
%d bloggers like this: