Hukumar NDLEA ta fara fitar da sunayen waɗanda ta ɗauka aiki

NDLEA Facebook

Hukumar yaƙi da hana ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta fitar da sunayen wadanda suka samu nasarar a ci gaba da daukar ma’aikata da ta ke yi.

Kakakin hukumar Jonah Achema,ne ya bayyana cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na kasar NAN a ranar Juma’a.

Mista Achema ya shawarci waɗanda suka nemi aikin da su ziyarci shafin hukumar na intanet www.ndlea.gov.org domin ganin ƙarin sunayen da aka wallafa bayan waɗanda aka tuntuba ta sakon karta kwana da kuma Email.

A cewarsa mutane da dama sun nemi wannan aiki a kuma matakai daban-daban, wasu ma har an kirasu domin su je a musu jarrabawa.

“Wadanda aka tuntunɓa su 5,000 za su je ma’aikatar CCNN da ke jihar Plateau domin tantance su tare da takardunsu, kuma za a fara ne tsakanin 10 ga watan Janairun da muke ciki zuwa 23 ga watan, za a rika fara aikin a kullum daga karfe 09:00 na safe.

“Za a raba masu neman aikin zuwa kashi hudu domin aikin tantancewa, domin tabbatar da an bi dokar da kuma ka’idojin wannan annoba ta Covid-19,” in ji Mista Achema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here