Hukumar NDLEA ta ce ta kama kwayoyin biliyan 10 a Kano da Legas

NDLEA

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wasu kwayoyi da suka kai darajar naira biliyan 10 a filayen jirgin saman Murlata Muhammed da ke Legas da kuma na Mallam Aminu Kano da ke jihar ta Kano.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar Femi Babafemi ya ce an gano kayan ne a cikin wani jirgin daukar kaya da ya taso daga Afrika Ta Afrika da kuma na Habasha.

A cewar sanarwar yayin wani bincike da jami’an hukumar suke yi an gano wasu abubuwa da ke cikin wata jaka da ake kira da Ghana-must-go.

“Yayin wata tattaunawa da aka yi da wadanda ake zargi, wani jami’i ya kara gano wasu mutane shida da ake zargi tare da wasu kaya da aka auna aka ga kwayoyi ne da suka kai nauyin kilogiran 24.05.

“Kazalika an akara kama wasu kayan masu nauyin kilogiram 1.25 wanda hakan yakai kayan da aka kama 25.3kg.

“Jirgin dai ya iso Najeriya ne ranar 16 ga wtaan Afrilun da muke ciki kuma an gudanar da binciken da ya kamata a kanshi,” in ji sanarwar.

An kuma kara kama irin wadannan kwayoyi a Kano da aka yi shirin fitar da su Manchester, wadanda suka kai nauyin kilogiram 36, hakan ya kai kayan da aka kama duka zuwa 63kg.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here