Daga Auwal Isah

An bukaci al’umma jihar Katsina su fahimta, tare da goya ma ayyukan hukumar KASROTA baya.

Shugaban kwamitin kafa hukumar Sani Aliyu Danlami ya yi wannan kiran a lokacin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a dakin taron sakatariyar jihar Katsina.

Kamar yadda ya bayyana, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari shi ne ya kafa kwamitin don ganin ya taimaka wurin kafa hukumar cikin nasara.

Sani Aliyu Danlami da ya samu wakilcin babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina Sulaiman Isyaku Safana, ya ce kwamitin ya cimma abubuwa da dama tun baya kafa hukumar.

Ya ce kwamitin ya ziyarci sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman, da sarkin Daura Umar Faruq Umar, da babban jojin jihar Katsina Mai shara’a Musa Danladi Abubakar, da kakakin majalissar dokokin jihar Katsina Tasi’u Musa Maigari, da kuma kafafen yada labarai, da dai sauransu.

Sun kuma kai ziyara makwabtan jihohin Katsina irinsu su Kaduna, Kano da kuma Bauchi don kara samu ilimin da za a yi amfani da shi wurin kankamar hukumar cikin nasara.

Sani Aliyu Danlami ya kara da cewa, nan da zuwa mako daya mai zuwa ne za a yaye jami’an hukumar 100 da aka gama ba horo, wanda gwamnatin jihar Katsina ta dauka aiki a cikin hukumar, inda kuma zasu fara aiki a ranar 1 ga watan Yunin wannan shekarar.

Shugaban kwamitin ya kuma ce, hukumar za ta gudanar da aikin wayar da kan al’umma na wata guda ba tare kama kowa ba don ganin an fahimci juna.

Idan dai za a iya tunawa, gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya sanya ma dokar da ta kafa hukumar hannu a ranar 27 ga watan Nuwanbar shekarar 2019.

Kuma hakan na zuwa ne bayan da majalissar dokokin jihar Katsina ta gama aikinta.

A nashi bangaren, shugaban hukumar KASROTAn AIG Danlami Yar’adua mai ritaya, ya yi kira ga masu ababen hawa da su goya ma hukumar baya don ganin ta cimma nasara a fadin jihar Katsina.

Danlami Yar’adua ya kuma yi alkawalin yin aikin ba tare da tsoro ko saurara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here