Advert
Home Sashen Hausa Hukumar EFCC Ta Gurfanar Da Wata Mata Kan Zambar N13m

Hukumar EFCC Ta Gurfanar Da Wata Mata Kan Zambar N13m

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati, EFCC, reshen Jihar Kano a ranar 16 ga Agusta, 2021, ta gurfanar da Rashida Ibrahim Usman a gaban Mai Shari’a Maryam Ahmed Sabo ta Babbar Kotun Jihar Kano da ke zaune a Milla Road, Bompai, Jihar Kano.

Jami’an Hukumar sun cafke wadda ake zargin ne bayan ƙorafin da wata Hajiya Wasila ta yi wanda a cikin watan Afrilun 2018 ‘yar uwarta, Pricia Shaaibu ta gabatar da ita ga wanda ake zargi tare da bayanan cewa ita’ ƴar kasuwa ce mai Alaƙa da kasuwanci. Da ake kira Golden Premier Club.

Daga baya, wadda ake zargin ta gayyaci mai ƙara zuwa Abuja inda ta bayyana mata cikakken bayanin kasuwancin. Wanda ya shigar da ƙarar ya nuna sha’awar kasuwancin kuma ya sanya jimlar Kudi Naira 13,780,000 (Miliyan Goma sha Ukku, da Ɗari Bakwai da Tamanin) an biya kuɗin ne ta hanyar asusun wanda ake ƙara wanda ke zaune a bankin Diamond Plc tare da asusun N0. 0099629622.

An karanto ma wadda ake ƙara, “cewa ke Rashida Ibrahim Usman wani lokaci a cikin shekarar 2018 a Kano, a ƙarƙashin ikon wannan Kotun Mai Girma, da nufin yin ha’inci, kun karɓi kuɗi Naira Miliyan goma sha uku da dubu ɗari Bakwai da tamanin daga asusun Hajiya Wasila.

Wadda ake tuhumar ta musanta zargin da ake yi ma ta.

Dangane da rokon da ta yi, lauyan masu gabatar da kara, Zarami Muhammad, ya roƙi kotun da ta tsare wadda ake ƙara a gidan yari tare da tsayar da ranar da za a fara shari’ar.

Lauyan da ke kare wacce ake ƙarar, Abdullahi Muhammad, ya sanar da kotun cewa ya shigar da Buƙatar neman belin wadda yake karewa, sannan ya bukaci kotun ta amince da belin ta.

Mai shari’a Sabo ya bayar da belin wadda ake tuhuma a kan kudi Naira Miliyan Biyu (N2,000,000) da mutum biyu masu tsaya ma ta.

Wadanda za su tsaya ma ta dole ne su kasance suna da kadarorin da ba za a iya gazawa ba ko kuma kadarorin da suka kai Naira Miliyan Biyar (5,000,000) a cikin Jihar Kano.

An daga shari’ar zuwa ranar 25 ga Oktoba, 2021, domin shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: