Advert
Home Sashen Hausa Hukumar binciken sararin samaniyar Amurika NASA zata kaddamar da aikin yin bandaki...

Hukumar binciken sararin samaniyar Amurika NASA zata kaddamar da aikin yin bandaki a sararin samaniyar.

The toilet is located inside a stall on the space station

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka Nasa za ta ƙaddamar da aikin yin banɗaki a sararin samaniya kafin a iya fara amfani da shi nan gaba a tafiya zuwa duniyar wata.

Banɗakin wanda zai lashe kuɗi dala miliyan 23, wanda ke zuƙo najasa daga jikin mutum, za a aika shi tashar sararin samaniya ta hanyar amfani da jirgin ruwan ɗaukar kaya.

Nasa ta ce famfunan da ke zuƙo abu na banɗakin an tsara shi ne ta yadda mata ƴan sama jannati za su ji daɗin amfani da shi, ba kamar tsohon tsarin ba.

An so a harba rokar da ke ɗauke da jirgin ruwan dakon kayan ne daga Tsibirin Wallops da ke Virginia a ranar Alhamis.

Amma shirin ya gamu da cikas minti uku kafin harbawar saboda matsalolin na’ura da aka samu.

Za a sake gwada harbawar a yau Juma’a da yamma idan har injiniyoyi suka gyara matsalolin da suka jawo tsaikon na ranar Alhamis.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WHAT SECTORS OF THE GLOBAL ECONOMY DID NIGERIA ENGAGE MORE IN LAST YEAR?

WHAT SECTORS OF THE GLOBAL ECONOMY DID NIGERIA ENGAGE MORE IN LAST YEAR? #PositiveFactsNG This infograph below shows us what sectors of the global economy Nigerian...

NEW INFRASTRUCTURE FOR THE NIGERIAN NAVAL BASE IN AKWA IBOM STATE!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/257872623095929/