A jiya ne shugaban karamar hukumar funakaye dake jahar gombe ya kaddamar da rushe gidan wani limami sakamakon huduba da yayi akan shugabanni.

Lamarin ya faru ne sakamakon kwatanta da shugaban nin da azzalumai da limamin yayi a lokacin hudubar jumaa Wanda hakan beyiwa shugaban karamar hukumar dadi ba.

Washe garin ranar asabar ne kuwa akaga cartapilla hade da jami’an tsaro sun dirarwa gidan liman inda suka ruguza gidan har kasa.

Munyi kokarin jin ta bakin chairman din amma abin yaci tura.

Amma da muka tuntubi limamin ta wayar tarho ya shaidawa wakilin mu tajuddeen koki cewa yana gida aka kawo masa takardar gayyata daga police station inda daga zuwansa aka dauki bayanansa aka kai shi kotu da laifin gini ba bisa ka’ida ba.

Limamin yakara da cewa alqali ya karanta min tuhuma ta inda nikuma na musanta amma duk da haka se aka hadani da ‘yan sanda tareda hukumar kula da gine-gine ta jahar gombe inda bamu tsaya ko ina ba se gidana Wanda a take aka rushe shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here