Shimfiɗa:
Alhaji Lamis Shehu Dikko gogagge ne a fannin da ya shafi tattalin arziƙi, gogaggen ma’aikacin banki, kuma mashahurin ɗan kasuwa.
A ɗaya gefen kuma basarake ne wanda yake riƙe da sarauta a masauratar Katsina ta Ajiyan Katsina.
Alhaji Lamis ya bayar da gagarumar gudummawa wurin ci gaban tattalin arziƙin Najeriya ta fannoni da yawa. Kuma gogaggen ɗan siyasa ne.
Alhaji Lamis Shehu Dikko mutum ne mai mu’amala cikin sakin fuska, mutum ne mai karamci, mutum ne mai zumunci da tausayi da kyautatawa mutane. Ya kasance jigo kuma bango a rayuwar mutane da yawa, mutum ne mai yawan kyauta da alheri. Ya taimaki mutanen da shi kan sa bai san yawansu ba.
Ya yi aiki na shekaru fiye 25 na banki. Babu in da ba a ji shi ba a shekara 25 da ya yi yana aikin banki, mutum ne mai cikakkiyar ƙwarewa kuma mai hangen nesa a harkar aikinsa, mutum ne mai aiki tuƙuru da gaske. Mutum ne mai gaskiya da riƙon amana.
Haihuwa:
An haife shi a Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa da ke jihar Katsina a cikin shekarar 1957.
Karatu:
Ya fara makarantar Firamare a Ɓatagarawa daga nan ya koma Jos sakamakon canjin wurin aiki da mahaifinsa ya samu, sai ya ci gaba da Firamare ɗin sa acan, daga baya kuma sai ya dawo Katsina in da ya kammala Firamare ɗin sa anan.
Bayan ya kammala Firamare sai ya ci gaba in da ya shiga makarantar sakandare da ake kira a wancan lokacin Government Secondary School Katsina wacce sunanta ya koma a yanzu Government College Katsina, anan makarantar ya yi sakandare har zuwa lokacin da ya kammala.
Bayan nan sai ya wuce ya tafi garin Zariya in da ya samu damar shiga College of Advanced Studies, bayan nan ya shiga jami’ar Ahmadu Bello in da ya fara karanta tattalin arziƙi (Economics).
Kafin ya kammala Jami’ar Ahmadu Bello sai ya tafi ƙasar Ingila in da ya shiga jami’ar Queen Mary’s College, University of London.
A wannan jami’a ta London anan ya kammala karatun digiri ɗin sa na ɗaya a tattalin arziƙi BSC Degree a Economics kuma ya fita da mafi kyawun sakamako in da ya fita da daraja ta farko (First Class).
Sannan ya yi karatu a Harvard Business School for Management Development.
Aiki:
Kafin tafiyarsa karatu Ingila ya yi aikin gidan rediyo na shekara ɗaya a Kaduna State Radio a matsayin mai shirya labarai da kuma abubuwan da suke faruwa a yau. Bayan dawowarsa daga Ingila ya yi aiki a jaridar Nigerian Standard a matsayin Sub-Editor.
Sannan ya koyar a makarantar College of Advanced Studies, Zaria in da ya koyar da tattalin arziƙi na shekara ɗaya a makarantar.
A shekarar 1986 ya shiga aikin banki, in da ya fara aiki a Habib Bank, ya yi shekara 12 ya na aikin, daga 1986 zuwa 1998.
Bayan nan sai ya haɗu da wasu abokan aikinsa kamar Alhaji Falalu Bello da Malam Adamu Bello da wasu suka haɗa team suka samo mutanen da suka zuba hannun jari a bankin Intercity Bank, a lokacin bankin jihar Neja ne, kuma suka kafa sabuwar hukumar gudanarwar bankin, kuma suka dawo da headquarter bankin Kaduna, in da ya fara da matsayin General Manager.
A shekarar 2001 ya zama Managing Director na Intercity Bank, kuma ya riƙe wannan muƙamin zuwa shekarar 2005.
Bayan nan sai aka yi haɗakar bankuna in da aka haɗa bankuna guda takwas, ciki har da Intercity Bank, in da sunan bankin ya koma Unity Bank.
Bayan an gama wannan haɗakar sai Lamis Dikko ya zama Executive Director na Unity Bank, ya riƙe wannan muƙamin daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2010 sannan ya yi ritaya.
Bayan ya yi ritaya saboda gogewarsa a ɓangaren aiki ya ci gaba da hulɗa da fannonin aikin banki.
Ya zauna a hukumar gudanarwar Enterprice Bank Limited.
Ya riƙe Non-Executive Director a Mutual Benefits Assurance Plc.
Ya riƙe Chairman na Legacy Pension Managers (PFA) Ltd.
Alhaji Lamis ya yi Executive Director na Commercial Banking a Unity Bank. Sannan kuma ya yi Chairman na hukumar gudanarwar Unity Bank.
Ya yi aiki a Governing Council Nigeria Stock Exchange.
Alhaji Lamis Dikko ya yi aiki a hukumar gudanawar kamfanoni masu zaman kan su da yawa.
Kuma shi ne Chairman na Infrastructure Bank Plc. Kuma shi ne Chairman na NICON Insurance Ltd.
SIYASA:
Ya fara siyasa ne tun daga makaranta, domin lokacin da yake College of Advanced Studies ya riƙe muƙamin Secretary General na ƙungiyar ɗalibai. Sannan da yaje jami’ar Ahmadu Bello ma ya riƙe Secretary General na ƙungiyar ɗaliban jami’ar.
Kuma ya yi takarar kujerar Sanatan Katsina ta tsakiya a shekarar 2015. Kuma ya na cikin jigo a jam’iyyar PDP ta ƙasa.
Iyali:
Alhaji Lamis Shehu Dikko ya na da mata da yara. Ɗaya daga cikin yaransa Adam Lamis Dikko shi ma kamar mahaifinsa ya karanci tattalin arziƙi (Economics) kuma ya fita da kyakkyawan sakamako na daraja ta farko (First Class).
Mutane da yawa sun yi wa Lamis Dikko kyakkyawan shaida musamman kan gaskiya da riƙon amana. Ga bayanan kaɗan daga cikin wasu manyan mutane a Najeriya;
Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Marigayi Malam Umaru Ƴar aduwa ya ce: Duk in da ake jagora, wato shugaba wanda za a yi aiki nagari to idan aka samu Lamis ba a sake neman wani. Ko kai
babba ne Lamis zai ce maka a’a idan kan hanyar rashin gaskiya ne, zai gaya maka yadda kai ranka ba zai ɓaci ba.
Marigayi Sarkin Katsina Kabir Usman ya ce: Ajiya a taƙaice amintacce kenan ga masarautarmu, amintaccen mutum shi ake ba sarautar Ajiya. Shi Matawalle aka wo mai kuɗi ya kai wa Ajiya.
Marigayi Ɗan Masanin Kano ya ce: Duk wanda ya san Lamis ya san shi da zumunci, duk mutumin da ya san Lamis ya san shi da kyautatawa mutane na unguwarsu da in da ya zauna, duk mutumin da ya san Lamis ya san shi da girmama manya, duk mutumin da ya san Lamis ya san shi da kyakkyawan alaƙa da masarauta, masarautar Katsina da Kano, duk wanda ya san Lamis ya san shi da gaskiya da riƙon amana, mutumin da ya yi aikin banki shekara da shekaru har yanzu ba mu ji laifinsa ba.
Daga Jaridar Labarai.ng
Rubutawa Ibrahim Imam Ikara