- Aya Primary School Funtua (1952)
Sunan Aya ya samo asali ne da sunan matar Sarkin Maska muhammadu Sani Wanda shine na 15 a jerin sarakunan kasar Maska Kuma yayi sarauta daga shekara ta 1832 zuwa 1865.
Ita Aya diya ce ga Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje,
Ummarun Dallaje yayi sarauta Katsina daga shekara ta 1807 zuwa 1835 Kuma yayanshi guda 4 ne sukayi sarauta bayanshi. - Gudindi Model Primary School Funtua (1937)
Sunan wannan makarata ya samo asali ne daga sunan Sarkin Maska Gudindi Wanda yayi sarauta daga shekara ta 1810 zuwa 1817 Kuma shine Sarki na 12 a jerin sarakunan kasar Maska. - Idris Girls Model Primary School Funtua (1986)
Sunan wannan makarata ya samo asali ne daga sunan Sarkin Maska Idris Sambo Wanda yayi sarauta daga shekara 1968 zuwa ta 1995 shine Sarki na 24 a jerin sarakunan kasar Maska, kuma shine mahaifin Sarkin Maska na yanzu Alh Sambo Idris Sambo da Kuma Hakimin Mairuwa Alh Sani Idris Sambo.
4.Sambo Primary School Funtua (1959)
Sunan wannan makarantar ya samo asali ne daga sunan Sarkin Maska Sambo Wanda yake mahaifi ga Sarkin Maska Shehu da Kuma Sarkin Maska Idris Sambo.
Sarkin Maska Sambo yayi sarauta daga shekara ta 1927 zuwa ta 1963 Kuma shine Sarkin Maska na 22
- Shehu Primary School Funtua (1956)
Sunan wannan makarantar ya samo asali ne daga sunan Sarkin Maska Shehu II Wanda yayi sarauta daga shekara ta 1963 zuwa ta 1968 Kuma shine Sarkin Maska na 23.
Sarkin Maska Shehu ya rike mukamin minista a zamanin Sardauna
Allah ya gafarta masu kuma ya albarkaci zuri’arsu baki daya ameen.
Gamarali #flashback
Source:
Katsina City News
Via:
Katsina City News