Hidden N19.3bn Kogi Salary Bail-Out Funds Returned to CBN

Hausa Translation:

Babban Bankin Najeriya Ya Karbi Wasu Kudade Da Aka Boye Kimanin Naira Biliyan Sha Tara Na Tallafin Albashin Ma’aikatan Jihar Kogi

Babban bankin Najeriya, CBN, ya tabbatarwa hukumar EFCC cewa ya karbi wasu kudade kimanin N19, 333,333,333.36 (Naira biliyan goma sha tara da miliyan dari uku da talatin da uku, da dubu dari uku da talatin da uku da dari uku da talatin da uku) wanda hukumar EFCC ta gano kuma ta kwato daga asusun tallafin biyan ma’aikatan jihar kogi albashi wanda suke shake a bankin Sterling.

Tabbatar da karbar kudin daga babban bankin tarayyar Najeriyar ya kawo karshen cece kuce da nuna yatsa da ma musantawa da gwamnatin jihar Kogi ke yi cewa babu wasu kudade da aka gano daga asusunta na tallafin biyan ma’aikata.

Babban bankin Najeriya a wata takardar mai lamba DFD/DIR/CON/EXT/01/099 mai dauke da kwanan wata tara na Nuwamba, 2021 ya bayyanawa shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa cewa ya karbi kudin.

Don karanta karashen labarin, ku ziyarci sashen intanet na EFCC a www.efccnigeria.org.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here