YANZU-YANZU

Hayaniya Ta Ɓarke A Zauren Majalisar Dattijai Kan Kudirin Kafa Hukumar Kula Da Soji

Hayaniya ta barke a zauren majalisar Dattijai ta Najeriya, kan kafa hukumar kula da sojoji.

Kudurin ya raba kan ‘yan Majalisar ne yayin da ake kokarin yi masa karatu na 2. Hayaniyar tsakanin wakilan APC ne dana PDP.

Yan PDP na son a kafa Hukumar ne saboda damar da kundin tsarin mulki ya baiwa majalisar ta kafata, yayin da ‘yan APC kuma ke zargin ana son kafa hukumar ne dan ragewa shugaban kasa karfin Iko.

Yan Majalisar APC, Ovie Omo-Agege, Abdullahi Adamu, Adamu Aliero da Mohammed Bulkachuwa sun kalubalanci kudirin. Yayin da na PDP, Emmanuel Bwacha, Chukwuka Utazi da James Manager suka goyi baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here